NiMet Ta Fadi Jihohin Arewa 18 da za a Yi Zafi Mai Tsanani, Ta Bayyana Dabarun Kariya

NiMet Ta Fadi Jihohin Arewa 18 da za a Yi Zafi Mai Tsanani, Ta Bayyana Dabarun Kariya

  • Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa za a fuskanci matsanancin zafin rana a Gombe da wasu jihohi 17 na Arewa
  • Hukumar ta ce zafin na iya kaiwa digiri 40 a ma’aunin Celsius daga ranar Asabar 12 ga Afrilu, tare da sauyin yanayi da zai janyo rashin jin daɗi
  • Baya ga haka, NiMet ta shawarci jama’a da su rika shan ruwa sosai, su guji rana da kuma kula da yara da tsofaffi a cikin yanayin da za a shiga

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da gargadi dangane da yiwuwar fuskantar matsanancin zafin rana a jihar Gombe da wasu jihohin Arewa.

Gargadin ya fito ne daga ofishin manajan hukumar a Gombe, Gayus Musa, inda ya bayyana hakan a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Najeriya ta hada kai da kasar Japan domin tallafawa manoma 500,000

zafin rana
NiMet ta ce za a yi zafin rana a jihohin Arewa. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Legit ta tattaro bayanai game da hasashen da hukumar ta yi a cikin wani sako da NiMet ta fitar a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta wallafa cewa NiMet ta ce yanayin zafin zai fara ne daga ranar Asabar, 12 ga watan Afrilu, kuma zai iya haifar da rashin jin daɗi ga mazauna yankunan da abin ya shafa.

Jihohin Arewa 18 da za a sha zafi

Hukumar ta bayyana cewa bayan kwanaki uku ana samun ruwa, yanzu ana sa ran samun hasken rana mai ƙarfi da iskar da za ta ƙara tsananta zafin.

Sanarwar hukumar ta ce:

“Yanayin zafin rana na iya kaiwa digiri 40 a Arewa. Jin zafin rana da rashin jin daɗi za su ƙaru,”

Gayus Musa ya bukaci al’umma da su ɗauki matakan kariya daga matsanancin zafin domin guje wa illar da zai iya janyo wa lafiya.

Jihohin da za su fuskanci zafin sun hada da Borno, Adamawa, Taraba, Gombe, Yobe, Bauchi, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Niger, Kogi, Nasarawa, Benue da Abuja.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, Nijar ta yi watsi da Faransanci, ta zabi Hausa a matsayin harshen ƙasa

Dabarun samun kariya daga zafin rana

Bayan fitar da sanarwar, hukumar NiMet ta ba mutane shawari kan yadda za su zauna lafiya a yanayin.

Jami'in hukumar ya ce:

“Ina shawartar jama’a su rika zama a wuraren da iska ke shiga, su rika sanya kaya masu sauƙin shaƙar iska, su sha ruwa mai yawa...
"Su guji fita tsakanin ƙarfe 12:00 na rana zuwa 3:00 na yamma kuma su nemi kariya daga rana.”

Musa ya ƙara da cewa ya kamata mutane su rika duba lafiyar yara da tsofaffi a lokacin zafin, domin su ne mafi rauni a irin wannan yanayi.

Rana zafi
An bukaci mutane su rika amfani da lema domin kare kansu daga zafi. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Ya kuma bukaci hukumomi da kungiyoyin masu ruwa da tsaki su ƙara wayar da kan jama’a game da haduran da ke tattare da zafin da hanyoyin kariya, domin kare lafiyar al’umma gaba ɗaya.

Gwamnati ta fara shirin daminar 2025

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta fara shirye shirye domin tunkarar daminar bana.

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya gana da jami'an kasar Japan a wani shiri na tallafawa manoma a Najeriya.

A hakadar da aka yi da Najeriya da Japan, za a tallafa wa manoma 500,000 domin samar da wadataccen abinci a daminar 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng