Ana Hasashen Saukar Farashin Mai bayan Dangote Ya Dawo Sayar da Fetur da Naira
- Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote ta koma sayar da fetur da Naira bayan dakatar da hakan na tsawon kwanaki 22
- Biyo bayan haka, farashin litar man fetur ya sauka daga N880 zuwa N865, wanda zai iya rage tsadar fetur a fadin Najeriya
- Ƙungiyar IPMAN ta ce sabon farashin na iya kawo ragin farashi ga jama’a, duk da cewa masu tsohon kaya suna tafka asara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matatar Dangote ta koma sayar da man fetur da Naira, lamarin da ke kara ƙwarin gwiwar cewa farashin fetur zai sauka a faɗin Najeriya.
Matakin da matatar Dangote ta dauka ya zo ne bayan an dakatar da sayar da mai da Naira tsawon kwanaki 22.

Source: Getty Images
A cewar rahoton jaridar Punch, matatar ta sanar da abokan hulɗar ta cewa yanzu za ta rika sayar da litar mai a kan N865, bayan ragin N15 daga tsohon farashin N880.
Sauyin farashin ya haɗa da kuɗin da hukumar NMDPRA ke karba, kuma ana sa ran zai sauƙaƙa farashin mai a kasuwa.
Fatan saukar farashin man fetur
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar dillalan mai masu zaman kansu (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce matakin zai rage tashin farashin fetur.
Chinedu Ukadike ya kara da cewa matakin zai ba ‘yan kasuwa damar samun isasshen kaya da saurin sayarwa.
Sai dai ya ce:
“Wasu daga cikinmu da suka saye man da tsohon farashi kafin wannan sauki, yanzu suna tafka asara.
"Duk da haka, muna maraba da sabon farashin da fatan komai zi daidaita.”
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban IPMAN, Hammed Fashola, ya ce wannan mataki abin maraba ne sosai kuma zai amfani ‘yan Najeriya.
Ya ce:
“Mun dade muna roƙon gwamnati da ta tabbatar da dorewar tsarin sayar da mai da Naira. Yanzu da aka dawo da shi, za mu samu sauƙin farashi.”
Gwamnati za ta karfafa matatun Najeriya
A ranar Laraba, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta bayar da umarnin aiwatar da cikakken tsarin sayar da danyen mai Naira da danyen mai da aka dakatar a baya.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan tsari ba na wucin gadi ba ne kuma an yi shi ne don tallafawa matatun mai na cikin gida.

Source: Facebook
Masani kan harkokin man fetur, Olatide Jeremiah, ya ce sauyin farashin Dangote ya haifar da gasa a kasuwar mai, kuma hakan zai amfani masu aiki da fetur gaba ɗaya.
Masu matatu sun yi hasashen saukar mai
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar masu matatun man fetur ta Najeriya ta ce akwai hanyoyin da za a bi wajen sauke farashin mai a Najeriya.
Kungiyar ta ce dawo da sayar da danyen mai wa matatun mai na cikin gida kamar matatar Dangote na cikin matakan.
Ta kara da cewa idan farashin danyen mai ya cigaba da karyewa a kasuwar duniya dole farashin man fetur zai ragu a Najeriya.
Asali: Legit.ng


