Sheikh Bello Yabo Ya Fadi Sirrin Alakarsa da Marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi

Sheikh Bello Yabo Ya Fadi Sirrin Alakarsa da Marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi

  • Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya bayyana alakar shekaru 30 da ya yi da marigayi Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi
  • Sheikh Bello Yabo ya ce Dr. Idris Dutsen Tanshi yana daya daga cikin malaman da suka fi ba shi kariya da taimako a rayuwarsa
  • Bayan ta'aziyyar da ya yi, Bello Yabo ya shawarci daliban marigayin su ci gaba da wa'azi da yin addu'a wa marigayin a ko da yaushe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Malaman addini a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya yi jawabi mai cike da tausayawa da tarihin zumunci dangane da rasuwar marigayi Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

Bello Yabo ya bayyana cewa sun shafe shekaru fiye da 30 suna tare da Dr Idris, yana mai cewa irin zumuncin ba ya yankewa ko bayan mutuwa.

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

Bello
Bello Yabo ya je Bauchi ta'aziyyar Dr Idris Abdulaziz. Hoto: Sheikh Bello Yabo|Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan Bello Yabo ne a cikin wani bidiyo da Dutsen Tanshi Majlis ya yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamai 2 da suka ba Bello Yabo gudumawa

Sheikh Bello Yabo ya ce akwai malamai biyu da suka ba shi gudummawa sosai a rayuwarsa har ya ji a ransa ba zai iya rama musu ba, ko da ya goya su a baya, ya je Makka ya dawo.

Wadanda ya ambata sune marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi da kuma Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya.

Ziyarar Idris Dutsen Tanshi Sokoto ta farko

Bello Yabo ya bayyana irin gudunmawar da Dr Idris ya bayar lokacin da aka kama shi a wata shari’a a Sokoto a shekarar 2004.

Ya ce jita-jita ta yadu cewa zai samu beli a ranar 1 ga Satumba 2004, lamarin da ya sa Dr Idris ya tayar da motoci daga Bauchi zuwa Sokoto domin taya shi murna.

Kara karanta wannan

Ana cikin karbar ta'azziya, iyalan Dutsen Tanshi sun sake gargadi kan wasiyyarsa

Ya ce ranar na daga cikin ranakun da suka fi tada hankalinsa a rayuwa, inda ya ga daruruwan mutane sun taru a kotu har ana zagin alkali.

A cewar Bello Yabo, saboda tashin hankali da aka shiga, ‘yan sanda sun zagaye kotun amma mutane suka zagaye su ko ta ina.

Bello Yabo ya ce:

'Ana cewa ba na tsoro, amma a ranar sai da na ji wani abu a raina,'

Malamin ya bayyana cewa marigayi Dr Idris yana wajen yana kallon duk abin da ke faruwa domin karfafa masa gwiwa.

Tinubu
Tinubu ya yi ta'aziyyar Dr Idris Abdul'aziz. Hoto: Bayo Onanuga|Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Twitter

Ziyarar Dr Idris Dutsen Tanshi Sokoto ta 2

Sheikh Bello Yabo ya kara da cewa bayan fitarsa daga gidan yari, an kashe Sheikh Dan Mai Shiyya a Sokoto, inda Dr Idris ya dawo domin jajanta musu, tare da yin wa’azi mai zafi a kofar gidansa.

Ya ce duk lokacin da wani ya soke shi, Dr Idris zai tsaya masa ko ya kira wanda ya yi maganar domin a warware zance.

Kara karanta wannan

Haduwar Izala: Sheikh Yusuf Sambo ya yi kira ga Jingir da Bala Lau

Bello Yabo ya tabbatar da cewa marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi ya kasance garkuwa a gare shi a lokuta da dama.

Shawara ga daliban Idris Dutsen Tanshi

A karshe, Bello Yabo ya shawarci daliban Dr Idris su ci gaba da aikinsa na yada ilimi da wa’azin Musulunci.

Ya bayyana niyyarsa ta dawowa Bauchi don gudanar da wa’azi na musamman mai taken “Waye Dr Idris” domin bayyana abubuwan da mutane ba su sani ba game da rayuwar marigayin.

Gwamnan Bauchi ya yi jimamin rashin Dr Idris

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ziyarci daliban marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi.

Bala Mohammed ya yi musu jajen rashin da suka yi tare da bayyana cewa marigayin ya kasance mai fadin gaskiya.

A karshe, gwamnan ya tabbatar da mika filin Idin Games Village ga daliban marigayin domin su cigaba da sallah a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel