Ministocin Tinubu 2 Sun Samu Saɓani kan Batun Tsawaita Lokacin NYSC zuwa Shekara 2

Ministocin Tinubu 2 Sun Samu Saɓani kan Batun Tsawaita Lokacin NYSC zuwa Shekara 2

  • Ministan Harkokin Matasa na ƙasa ya ce babu bukatar tsawaita lokacin aikin matasa masu yi wa kasa hidima watau NYSC
  • Ayodele Olawande ya ce kamata ya yi a yi wa shirin NYSC garambawul ta yadda za a rika horar da matasa su dogara da kansu
  • Wannan dai na zuwa ne bayan ministan ilimi, Olatunji Alausa ya bukaci a mayar da shirin NYSC shekara biyu a maimakon guda

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan harkokin matasan Najeriya, Kwamared Ayodele Olawande ya saɓawa tunanin ministan ilimi, Olatunji Alausa na tsawaita aikin bautar kasa (NYSC) zuwa shekaru biyu.

Olawande ya bayyana cewa kamata ya yi a bar aikin yi wa ƙasa hidima watau NYSC shekara ɗaya amma a mayar da hankali wajen horar da matasa su dogara da kansu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ba da mamaki, ya ce ya shirya shiga zanga zangar Matasa a Najeriya

Ministan matasa, Ayodele Olawande.
Ministan matsa ya ce babu bukatar tsawaita wa'adin yi ƙasa hidima Hoto: @fmydNG
Asali: Twitter

Ministan ya yi wannan furuci ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wurin taron shekara-shekara da NYSC ta saba shiryawa a Abuja, in ji Daiy Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministoci sun yi saɓani kan shirin NYSC

Ayodele Olawande, ya bayyana cewa zai fi kyau a bar aikin yi wa kasa hidima shekara guda muddin za a mayar da hankali wajen ba matasa horo da kwarewa.

A cewarsa, idan matasa suka samu horo da gogewa yadda ya kamata, za su iya kirkiro ayyukan yi da bunkasa rayuwarsu bayan kammala aikin NYSC.

A baya-bayan nan, Ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ya bukaci a tsawaita shekarun hidimar kasa daga daya zuwa biyu.

Ya ce hakan zai ba da damar fadada shirin koyon sana’o’i da horon kasuwanci na NYSC ga matasa masu yi wa ƙasa hidima.

Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da hukumar NYSC ta fitar a baya bayan nan, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Za a tsawaita shirin NYSC a Najeriya?

Sai dai Olawande ya ce abin da yafi dacewa shi ne a kirkiri wani tsarin horaswa da zai bai wa ’yan bautar kasa damar samun kwarewa ta musamman da za ta taimaka musu su samu aiki ko su zama masu dogaro da kai.

“Yanzu haka, mafi yawan matasa suna kallon NYSC a matsayin lokacin da za su yi wa kasa hidima.
Yan bautar kasa.
Abin da ya kamata a yi wa ƴan bautar kasa a Najeriya Hoto: NYSC
Asali: Twitter

Amma da za su samu takardun shaida da horon da za su amfana da shi bayan kammala aikin, hakan zai fi yi musu amfani fiye da abubuwan kishadi da ake yi a sansanonin horaswa,” in ji shi.

Olawande ya kara da cewa dole ne a sake fasalin tsarin NYSC idan ana son ganin sauyi mai amfani.

“Ba wai ina cewa ba a yin abin kirki ba ne, amma dole ne mu canza dabaru idan muna so mu samu sababbin sakamako,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi halin da yake ciki bayan cewa ya yanki jiki ya fadi, an tafi da shi Faransa

Minista zai iya shiga zanga-zanga a Najeriya?

A wani labarin, kun ji cewa yayin da matasa suka fara fitowa kan tituna a wasu sassan Najeriya, Kwamared Ayodele Olawande ya ce rashin lokaci ne ya hana shi shiga zanga-zanga.

Ministan ya gargaɗi matasan da ke wanna zanga-zanga da su guji tayar da hankula ko lalata kyayyakin gwamnati.

Ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta hana su ƴancin yin zanga-zanga ba amma dai kofarta a buɗe take ta saurari kokensu ta hanyar lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262