Abin da Ya Faru tsakanin Daliban Dutsen Tanshi da Gwamnan Bauchi wajen Ta'aziyya

Abin da Ya Faru tsakanin Daliban Dutsen Tanshi da Gwamnan Bauchi wajen Ta'aziyya

  • Gwamna Bala Mohammed ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalai da daliban marigayi Sheikh Idris Abdulaziz a Bauchi
  • Bala ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon malami mai tsayawa kan gaskiya da bin koyarwar addinin musulunci
  • Gwamna Bala Mohammed ya dauki alwashin mika filin idi na Games Village domin amfanin daliban marigayin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya nuna alhini matuka kan rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

Gwamnan ya kai ziyarar tare da tawagar manyan jami’an gwamnati zuwa gidan marigayin domin mika ta’aziyya ga iyali da mabiyansa.

Bauchi
Gwamnan Bauchi ya je ta'aziyyar Dr Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sakon da hadiminsa, Lawal Muazu Bauchi ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan Dusten Tanshi, Pantami ya sanar da rasuwar babban malamin Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ziyarar, gwamnan ya ce ya zo ne a madadin kansa, iyalinsa, gwamnatin Bauchi da daukacin al’ummar jihar domin taya su jimamin babban rashi.

Gwamnan Bauchi ya yabi Dutsen Tanshi

Yayin ta'aziyyar, gwamna Bala ya ce Sheikh Dr Idris ya kasance malami jarumi wanda ya tsaya tsayin daka wajen yada sahihin ilimin addini, da adalci da bin doka.

Ya ce jihar Bauchi ta yi babban rashin jagora mai hikima, wanda koyarwarsa ta yi tasiri a rayuwar dubban mutane.

Gwamnan ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa, ya sa shi cikin Aljannal Firdausi tare da baiwa iyalai da mabiyansa hakurin jure rashin.

Maganar filin Idi na Games Village a Bauchi

A lokacin ziyarar ta’aziyyar, Gwamna Bala ya dauki alwashin gyara filin idi na Games Village domin mika shi daliban marigayi Dr Idris.

Ya bayyana cewa wannan alkawari yana da muhimmanci domin kara faranta zukatan mabiyan marigayin da kuma ci gaba da ayyukan da ya gada.

Kara karanta wannan

'Allah maka albarka': Bidiyon marigayi Albany na zuba addu'o'i ga Dutsen Tanshi

Haka kuma, ya bayyana cewa ya yafe duk wani sabani da ya taba shiga tsakaninsa da marigayin a baya.

Martanin daliban Dr Dusten Tanshi

A madadin iyalan marigayin da al’ummar Musulmai, Malam Yau da Alhaji Shehu Barau Ningi sun nuna farin ciki da godiya bisa ziyarar da gwamnan ya kai musu.

Shehu Barau ya jaddada cewa marigayin ya dade yana fatan samun filin idi na Games Village, don haka alkawarin Gwamna Bala ya zo daidai da burinsa.

Gombe
Gwamnanonin Arewa sun yi ta'aziyyar Dr Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Sun yi addu’a ga Allah da ya saka wa Gwamna Bala da alkhairi bisa karamcin da nuna wajen yin jaje ga iyalan malamin da dalibansa.

Ziyarar ta kasance mai cike da jimami da addu’o’i, inda jama’a suka hadu domin tunawa da marigayi Sheikh Idris Abdulaziz.

Sheikh Yahya Harun ya rasu a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Yahya Harun ya kwanta dama.

Kara karanta wannan

'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi

Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa an yi babban rashi a cikin sakon ta'aziyyar da ya fitar bayan rasuwar babban malamin.

Sheikh Yahaya Harun ya kasance cikin 'yan Najeriya da suka samu damar karatu a jami'ar Musulunci da ke Madina tun a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel