Matasa Sun Rikita Abuja da Zanga Zanga, an Fara Harba Barkonon Tsohuwa
- Tarin masu zanga-zanga sun fito tituna a biranen Abuja da Lagos duk da gargadin da ‘yan sanda suka yi a karshen mako
- ‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja yayin da Omoyele Sowore da Deji Adeyanju ke jagorantar gangamin
- Rundunar ‘yan sanda ta ce lokacin da masu zanga-zangar suka zaba ya ci karo ranar bikin ‘yan sanda na kasa na 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A safiyar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025, jama’a suka fito domin gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Najeriya, ciki har da Abuja da Lagos.
Zanga-zangar, wacce kungiyar Take-It-Back Movement ta shirya, na kokarin jawo hankalin gwamnati kan halin matsin rayuwa da zargin kara danniya da ake yi wa ‘yan kasa.

Asali: Getty Images
Daya daga cikin jagororin zanga zangar, Omoyele Sowore ya wallafa a shafinsa na X cewa 'yan sanda sun tarwatsa su a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ‘yan sanda ta fitar da sanarwa tana gargadin kada a gudanar da zanga-zangar, duba da cewa ranar Litinin din ta zo daidai da bikin Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa.
Sowore da Deji sun fita zanga zanga a Abuja
A babban birnin tarayya Abuja, an ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, da lauya mai fafutuka, Deji Adeyanju, suna jagorantar masu zanga-zangar a yankin Maitama.
Punch ta wallafa cewa ‘yan sanda sun yi kokarin tarwatsa su da borkonon tsohuwa, inda hakan ya jefa jama’a cikin rudani, amma hakan bai hana su ci gaba da bayyana korafinsu ba.

Asali: UGC
An tarwatsa masu zanga-zanga a Fatakwal
A Jihar Rivers kuwa, masu zanga-zanga sun fara taruwa a filin Isaac Boro da ke Port Harcourt, amma kafin su fara tafiya, ‘yan sanda sun tarwatsa su.
Hakanan a birnin Ikeja na jihar Lagos, wasu gungun matasa sun fito dauke da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce irinsu “Bamu da issasshen 'yanci” da “A daina danniya”.
‘Yan sanda sun ce ana son bata musu suna
A sanarwar da kakakin ‘yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ya bayyana cewa zanga-zangar yunkuri ne na bata suna da sauya hankalin jama’a daga girmama aikin ‘yan sanda.
Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Ko da yake muna goyon bayan ‘yancin jama’a na yin zanga zanga, gudanar da hakan a ranar bikin Ranar ‘Yan Sanda na nuna wata manufa da ke da karkatacciyar niyya.”
Korafe-korafen masu zanga-zanga
A cewar shugaban kungiyar Take-It-Back Movement na kasa, Juwon Sanyaolu, zanga-zangar ta kunshi bukatar sauyin siyasa da saukin rayuwa ga ‘yan kasa.
Sun zargi gwamnati da amfani da dokar laifuffukan yanar gizo wajen danne ‘yancin jama’a da kuma gazawa wajen shawo kan hauhawar farashi da tabarbarewar tsaro, musamman a Rivers.
An kwantar da tarzoma a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa ta kwantar da hankula a jihar Bauchi.
Kakakin 'yan sanda na jihar ya bayyana cewa an samu wani hargitsi a unguwar Jahun bayan da wani limami ya yi mummunar magana kan Dr Idris Dutsen Tanshi.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya bayyana cewa hakan bai kamata ya fito daga malaman addini ba kasancewar su ne jagororin al'umma.
Asali: Legit.ng