'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Tunkaro Birnin Damaturu? Gwamnati Ta Yi Bayani

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Tunkaro Birnin Damaturu? Gwamnati Ta Yi Bayani

  • Gwamnatin jihar Yobe ta fito ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun tunkaro birnin Damaturu
  • Mai ba Gwamna Mai Mala Buni shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam, ya fito ya musanta rahotannin
  • Birgdiya Janar Dahiru Abdulsalam ya bayyana rahotannin a matsayin na.ƙarya waɗanda babu ƙamshin gaskiya a cikinsu
  • Ya buƙaci al'ummar jihar musamman mazauna birnin Damaturu da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta yi magana kan wani rahoto da ya yaɗu a kafafen sada zumunta kan shigowar ƴan ta'addan Boko Haram birnin Damaturu.

Gwamnatin jihar Yobe ta ƙaryata rahoton wanda ke cewa ƴan ta’addan Boko Haram suna matsowa kusa da Damaturu, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kashe kashe a Plateau, ya dauki muhimmin alkawari

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamnatin Yobe ta musanta batun shigowar 'yan ta'addan Boko Haram birnin Damaturu Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Gwamnatin Yobe ta musanta batun shigowar ƴan Boko Haram

Mai ba gwamnan jihar Yobe shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ya musanta batun a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, mai cike da ruɗani, inda ya danganta shi da aikin masu tayar da zaune tsaye a jihar.

Rahoton da ake iƙirarin na sirri ne an yi masa taken, 'gargaɗin gaggawa kan tsaro' ya yaɗu a intanet, inda ake cewa wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun tunkaro birnin Damaturu.

A cewar Dahiru Abdulsalam, wannan gargaɗin bai fito daga ofishinsa ba, ƙarya ne kuma ya kamata a yi watsi da shi baki daya domin ba shi da wata madogara.

An jawo hankalin jama'a

Ya buƙaci jama’a, musamman mazauna birnin Damaturu, da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba.

Kara karanta wannan

Ruwa ya yi gyara: Gidaje sama da 70 sun yi fata-fata a Filato

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamnatin Yobe ta ce ba gaskiya ba ne batun 'yan ta'adda sun tunkaro birnin Damaturu Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Dahiru Abdulsalam ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin jihar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Ya kuma yi gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya da ka iya haddasa firgici maras amfani a cikin al’umma.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na cikin shiri sosai, suna ci gaba da lura da sanya ido domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Yobe

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makanai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Yobe da ke Aewacin Najeriya.

Ƴan ta'addan na Boko Haram sun hallaka wani ɗan sa-kai a harin da suka kai a garin Gujba da ke jihar.

Miyagun ƴan ta'addan sun kuma lalata shaguna takwas tare da ƙona shaguna 12 a harin da suka kai cikin tsakar dare a garin.

Majiyoyi sun bayyana cewa.ƴan ta'addan sun riƙa shiga gida-gida suna neman ƴan sa-kai domin su hallaka su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng