Shugaba Tinubu Ya Fusata kan Kashe Kashe a Plateau, Ya Dauki Muhimmin Alkawari

Shugaba Tinubu Ya Fusata kan Kashe Kashe a Plateau, Ya Dauki Muhimmin Alkawari

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan hare-haren da ƴan bindiga suka kai a jihar Plateau
  • Mai girma Bola Tinubu ya jajantawa gwamnatin jijar da Gwamna Caleb Mutfwang kan mummunan ta'addancin da miyagun suka tafka
  • Ya umarci jami'an da su tabbatar sun zaƙulo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci mai tsanani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin cewa za a kama ƴan bindigan da suka kashe mutanen wasu ƙauyuka a jihar Filato.

Ƴan bindigan sun kai hari kan wasu ƙauyuka a jihar, inda suka kashe sama da mutane 50 tare da lalata dukiyoyi.

Tinubu ya yi Allah wadai da kashe-kashe a Plateau
Shugaba Tinubu umarci jami'an tsaro su zakulo wadanda suka kashe mutane a Plateau Hoto: @CalebMutfwang, @DOlusegun
Asali: Twitter

Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya bayyana a cikin wata sanarwa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Jami'an tsaro sun cafke mai safarar kayayyaki ga rikakkun 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi alhini kan kashe-kashe a Plateau

Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnatin jihar Plateau da Gwamna Caleb Mutfwang, kan mummunan lamarin da ya auku.

Mai girma Bola Tinubu ya kuma buƙaci al’ummomin da lamarin ya shafa su haɗa kai da hukumomi da jami’an tsaro ta hanyar ba da bayanai domin a kama masu laifin da kuma kare lafiyar jama’a.

Ya tabbatarwa Gwamna Mutfwang samun cikakken goyon bayansa wajen kawo ƙarshen wannan mummunan kashe-kashe da ke faruwa a Plateau.

Tinubu ya kuma bayar da umarni ga hukumar NEMA da ta haɗa kai da hukumomin jihar domin tallafawa wadanda lamarin ya rutsa da su tare da samar da agajin gaggawa ga ƙauyukan da aka kai wa hari da waɗanda suka jikkata.

Wane umarni Tinubu ya ba da?

"NEMA za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar domin tabbatar da cewa al’ummomin da abin ya shafa sun farfaɗo da kuma ci gaba da rayuwa."

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

"Rahoton wani sabon hari da ƴan bindiga marasa imani suka kai kan wasu ƙauyuka a jihar Plateau ya tayar min da hankali matuƙa.Wannan hari kan fararen hula d aba su ji ba, ba su gani ba abin Allah-wadai ne."
"Na bai wa hukumomin tsaro umarni su bi sawun waɗannan miyagu, kuma za su fuskanci tsauraran hukunci idan aka kama su."
"Wannan jerin hare-haren da ake kai wa lokaci-lokaci ba su da gurbi a cikin ƙasar mu a daidai wannan lokacin da muke bakin ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da doka a kowane yanki na Najeriya."
Bola Ahmed Tinubu
Tinubu ya yi.alhini.kan kashe.kashe.a.Plateau Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook
"Wannan mummunan lamari ba zai hana mu ci gaba da ƙoƙarin kare rayukan ƴan ƙasa ba. Maimakon hakan, za mu ƙara azama wajen kawar da duk wasu miyagu a duk inda suke fakewa a cikin ƙasar nan."
"Zuciyarmu da addu’o’inmu na tare da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma duk waɗanda lamarin ya shafa a wannan harin na ban takaici. Babu wata al’umma da ya kamata ta fuskanci irin wannan masifa."

Kara karanta wannan

Ruwa ya yi gyara: Gidaje sama da 70 sun yi fata-fata a Filato

"Dole ne mu hada kai gaba daya domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ina kira ga duk ƴan Najeriya ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko jam’iyya ba, da su rungumi zaman lafiya, su guji ɗaukar fansa."

- Shugaba Bola Tinubu

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wani gari mai suna Riwi da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Ƴan bindigan a yayin harin, sun hallaka.mutane 10.waɗanda ba du ji ba, ba su gani ba da ke zaman makoki.

Miyagun waɗanda harin cikin dare sun buɗewa mutanen wuta ne lokacin da suke zaman makokin wani mutum da ya rasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel