Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Rasu Yana Kusa da Cika Shekara 90
- Mutuwa ta ratsa jihar Oyo inda aka yi rashin ɗaya daga cikin waɗanda suka taɓa riƙe ragamar harkokin mulkin jihar da ke yankin Kudu maso Yamma
- Tsohon gwamnan jihar Oyo, Dr. Omololu Olunloyo, ya yi bankwana da duniya da safiyar ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025
- Marigayin wanda ya taɓa zama shugaban farko na kwalejin fasaha ta Ibadan ya rasu ne ƴan kwanaki kaɗan kafin cikarsa shekara 90 a duniya
- Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamai daban-daban ciki har da na sarautun Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Tsohon gwamnan jihar Oyo, Chief Omololu Olunloyo, ya rasu ƴan kwanaki kaɗan kafin cikarsa shekaru 90 da haihuwa a duniya.
Tsohon gwamnan, wanda kuma shi ne Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife, ya rasu ne da safiyar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.

Asali: Twitter
Rasuwarsa ta tabbata ne cikin wata sanarwa da Oladapo Ogunwusi, ya sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Oyo ya rasu
Dr. Olunloyo, wanda ke riƙe da sarautun gargajiya na Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife, mutum ne da ake girmamawa sosai kuma ya yi fice a harkar hidimtawa jama’a da aikin gwamnati.
Shi ne shugaban farko kwalejin fasaha ta Ibadan, da kuma shugaban kwalejin fasaha ta jihar Kwara, tare da wasu muhimman muƙamai da dama da ya riƙe a rayuwarsa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
"Cikin zuciya mai cike da baƙin ciki amma tare da godiya ga Ubangiji, muna sanar da rasuwar Dr. Victor Omololu Olunloyo, tsohon gwamnan jihar Oyo, masanin lissafi da injiniya, kuma kwararren ma’aikacin gwamnati, ƴan kwanaki kafin cikarsa shekaru 90 da haihuwa."
“Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife, Dr. Olunloyo, shi ne shugaban farko na kwalejin fasaha ta Ibadan da kuma kwalejin fasaha ta jihar Kwara, tare da sauran muhimman muƙamai da ya riƙe."
"Tarihinsa na kwashe tsawon lokaci wajen hidimar da ya yi wa ƙasa da al’umma abin alfahari ne ga iyalansa da abokansa, duk da yake muna cikin alhinin rashinsa."
“Iyalin Olunloyo za su yaba da fahimtar ƴan jarida da al’umma yayin da suke shirin shirya masa jana’iza ta kirki.”
- Oladapo Ogunwusi
Shugaban APC a Kogi ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami a jihar Kogi bayan rasuwar ɗaya daga cikin shugabannin jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
Alhaji Suleiman Omika Mohammed wanda shi ne shugaban jam'iyyar APC a shiyyar Kogi ta Gabas ya koma ga mahaliccinsa yana da shekara 45 a duniya.
Marigayin ya rasu ne a gidansa da ke birnin Lokoja, babban birnin jihar a cikin wani yanayi na ban al'ajabi wanda ya ɗaurewa mutane kai.
Mataimakin gwamnan jihar Kogi, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai da ƴan uwan marigayi kan babban rashin da suka yi.
Asali: Legit.ng