Dubu Ta Cika: Jami'an Tsaro Sun Cafke Mai Safarar Kayayyaki ga Rikakkun 'Yan Ta'adda

Dubu Ta Cika: Jami'an Tsaro Sun Cafke Mai Safarar Kayayyaki ga Rikakkun 'Yan Ta'adda

  • Jami'an tsaro masu yaƙi da miyagun ƴan bindiga sun samu nasara a ƙoƙarin da suke yi na samar da tsaro a jihar Zamfara
  • Haziƙan jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara sun samu nasarar cafke wani mai safarar kayan sanyi ga ƴan ta'adda
  • Wanda ake zargin an cafke shi ne ɗauke da kayayyakin lokacin da yake yunƙurin kai su ga ƴan ta'addan da suka fitini jama'a
  • Bayan ya shiga hannu, za a miƙa shi ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike domin gurfanar da shi a gaban kotu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun kama wani wanda ake zargi da laifin kai kayayyaki ga ƴan bindiga mai suna Ashiru Jijji.

Jami'an tsaron sun cafke Ashiru Jijji ne bisa zargin kai kayan sha da sauran kayan abinci ga ƴan bindiga da ke aikata ta’addanci a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun samu gagarumar nasara

Jami'an tsaro mai safarar kayayyaki ga 'yan bindiga a Zamfara
Jami'an tsaro sun kama mai safarar kayan sanyi ga 'yan bindiga a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke mai safarar kayayyaki ga ƴan ta'adda

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa jami'an rundunar Askarawan Zamfara ne suka cafke wanda ake zargin.

Jami'an tsaron sun cafke Ashiru Jijji ne yayin wani sintiri da suka saba gudanarwa a ɗaya daga cikin wuraren da ake fama da hare-haren ƴan bindiga.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana aiki a matsayin mai kai kayayyaki, inda ya kai lemu da sauran kayan amfani zuwa maboyar ƴan ta’adda a cikin dazukan da suke ɓuya.

“Mun kama shi a yayin da yake jigilar katan-katan na lemu da wasu kayan masarufi. Lokacin da muka yi masa tambayoyi, ya amsa cewa kayan na ƴan bindiga ne da ya saba kai musu a kai a kai."

- Wata majiya

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kashe kashe a Plateau, ya dauki muhimmin alkawari

Za a miƙa wanda ake zargin wajen hukumomi

Yanzu haka Ashiru Jijji yana hannun jami’an tsaro, kuma ana shirin mika shi ga hukumomin tsaro da suka dace domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

Ashiru Jijji ya bayyana cewa kayayyakin ya yi niyyar kai su ne ga wasu riƙaƙƙun ƴan bindiga masu suna Ali da Inuwa.

Ya bayyana cewa yana ɗauke da kayan sanyi irinsu Lemun Maltina, Fearless da Seven Up.

Askarawan Zamfara na ƙoƙari

Wani mazaunin jihar Zamfara, Jamilu Abdullahi, ya bayyana cewa jami'an rundunar Askarawan Zamfara na ƙoƙari wajen samar da tsaro.

"Suna ƙoƙari sosai wajen aikin samar da tsaro kuma muna yaba musu. Muna fatan Allah ya ci gaba da ba su kariya."
"Allah ya ci gaba da tona asirin duk masu hannu a matsalar tsaron da muke fama da ita."

- Jamilu Abdullahi

Ƴan sanda sun fatattaki ƴan ta'adda

Kara karanta wannan

2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Benue sun samu nasarar ceto wasu fasinjoji da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.

Ƴan bindigan ɗauke da miyagun makamai sun tare matafiyan ne yankin ƙaramar hukumar Otukpo sannan suka kora su zuwa cikin daji.

Jami'an ƴan sandan tare da ƴan sa-kai sun ɗauki matakin gaggawa ta hanyar bin sawun ƴan bindigan sannan suka yi artabu da su.

Bayan artabun da aka yi, ƴan sandan sun fatattaki ƴan bindigan sannan suka samu nasarar ceto fasinjojin da suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng