'Dalilin Gwamnatin Kano na Sake Nada Dr Aliyu a Matsayin Sarkin Gaya,' Inji Abba

'Dalilin Gwamnatin Kano na Sake Nada Dr Aliyu a Matsayin Sarkin Gaya,' Inji Abba

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an mayar da Sarkin Gaya kan kujerarsa saboda jajircewarsa, da mika wuya ga Allah
  • Ya yaba wa Sarkin Gaya, Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, kan yadda ya nuna tawali'u da dogaro ga kaddarar Allah lokacin da aka tube shi
  • Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa za ta daga darajar Gaya, kuma tuni aka tura injiniyoyi domin fara ayyukan raya al'umma da kasa a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana gaskiyar dalilin da ya sa gwamnatinsa ta mayar da Sarkin Gaya kan kujerarsa.

Gwamna Abba ya ce an maryar da sarkin ne saboda irin jajircewarsa, tawali'u da kuma mika wuya ga hukuncin Allah a lokacin da aka tube rawaninsa.

Gwamna Abba ya yi magana da Sarkin Gaya ya kai masa ziyarar barka da Sallah a Kano
Gwamna Abba ya fadi dalilin mayar da sarkin Gaya kan karagarsa. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Abin da Sarki Sanusi II ya faɗa wa Gwamma Abba bayan ya yi hawan Sallah a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Abba na mayar da Sarkin Gaya kan mulki

A cewar Gwamna Yusuf, Sarkin Gaya, Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, shugaba ne da ya amshi kaddararsa cikin natsuwa, hakuri da dogaro ga hukuncin Ubangiji.

Yayin da yake yabawa Sarkin Gaya kan yadda ya dauki tube shi cikin tawali’u, gwamnan ya ce:

“Sarkin Gaya ya mika wuya ga hukuncin Allah lokacin da aka tube shi. Bai yi gardama ko nuna adawa ba; sai dai ya rungumi lamarin cikin imani, ya kuma dogara ga Allah."

Gwamnan ya ce irin wannan dabi’ar juriya da tawali’u ta zama dalilin da ya sa aka dawo da shi kan karagarsa, a lokacin da aka nada sababbin sarakuna.

Gwamnan Kano zai daga darajar Gaya

Gwamna Yusuf ya kara da cewa gwamnatinsa na da niyyar inganta ci gaban masarautar Gaya, inda ya bayyana cewa ana kan aiki don gyara muhimman ababen more rayuwa a yankin.

Kara karanta wannan

'Mu na zaman makoki, su na hawan Sallah,' Sarki Sanusi ya fusata wasu

Ya ce tuni aka tura tawagar injiniyoyi domin tantance hanyoyi da wasu gine-gine masu muhimmanci da ake bukata, inda ake shirin fara aikin gina su nan ba da jimawa ba.

A cewar Gwamna Abba Yusuf:

“Gwamnatinmu za ta sauya fasalin Gaya zuwa birni na zamani. Za mu fara da hanyoyin shiga kauyuka, sannan mu gina magudanan ruwa da gadoji domin kare ambaliya."

Ya ce wannan na daga cikin babban shirin gwamnatinsa na bunkasa masarautu gaba daya a jihar Kano.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na da cikakken goyon baya ga masarautu saboda rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya, hadin kai da kuma kare al’adun gargajiya.

Sarkin Gaya ya mika godiya ga Gwamna Abba

Sarkin Gaya, Dr Aliyu ya yi godiya ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Kano: Lokacin da Gwamna Abba Yusuf ke mika sandar girma ga Sarkin Gaya. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Twitter

A nasa bangaren, Sarkin Gaya, Dr. Aliyu Abdulkadir, ya nuna godiya matuka ga gwamna bisa amincewa da shi da kuma goyon bayan da yake ba shi.

Dr. Aliyu ya sha alwashin yin aiki kafada da kafada da gwamnati domin ci gaban masarautar da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gaya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sarkin Kano, Sanusi II ya ture umarnin 'yan sanda, ya yi Hawan Nasarawa

Matakin da gwamnan Kano ya dauka na mayar da Sarkin Gaya ya jawo yabo daga jama’a, inda suka ce hakan na nuna cewa hakuri, tawali’u da aminci na da matukar muhimmanci a shugabanci da zaman lafiyar al’umma.

Abba ya mika sandar girma ga Sarkin Gaya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sandar mulki ga Sarkin masarautar Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir.

Bayan rushe masarautun Kano a 2024, Gwamna Abba ya amince Dr. Aliyu ya ci gaba da zama a kan kujerar mahaifinsa, marigayi Ibrahim Abdulkadir.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.