Peter Obi Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Sauyin da Zai Kawo da Shi ne Shugaban Kasa
- Peter Obi wanda ya nemi shugabancin Najeriya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar LP a zaɓen 2023, ya caccaki mulkin Shugaba Bola Tinubu
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya soki Tinubu kan yadda yake tafiyar da manufofin gwamnatinsa a ɓangaren tattalin arziƙi
- Obi ya nuna cewa da shi ne shugaban ƙasa, da ya kawo muhimman sauye-sauye a cikin shekaru biyu da hawa kan karagar mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Peter Obi ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rashin sanin ya kamata wajen aiwatar da manufofin tattalin arziƙi.

Asali: Facebook
Peter Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise News a ranar Talata, 1 ga watan Afirilu 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya soki manufofin gwamnatin Tinubu
Peter Obi ya kuma soki matakin Shugaba Tinubu na sakin Naira sakaka ba tare da ƙasar nan na samar da muhimman kayayyaki da kanta ba.
Ya kuma soki yadda Tinubu ya ƙara yawan bashin ƙasar nan da kuma kuɗin da ake kashewa wajen biyan bashi, wanda ya ce ya fi kasafin kuɗin muhimman ɓangarori kamar kiwon lafiya da ilmi.
Obi ya jaddada cewa, idan da shi ne shugaban ƙasa, ƙasar nan za ta shaida gagarumin ci gaba cikin shekaru biyu, domin zai zuba jari a fannin samar da ayyukan yi, wanda hakan zai bunƙasa tattalin arziƙi.
Wane sauyi Peter Obi zai kawo?
"Shugaban da ke kan kujerar a yau, shekaru nawa ya yi? Shekaru biyu, ka duba halin da ake ciki. Wannan yana nufin ana iya canza abubuwa cikin shekaru biyu."
"Wato idan da ni ne a wurin, da an ga canji mai yawa a muhimman ɓangarori. Da na fuskanci cin hanci da rashawa kai tsaye, sannan da na rage yawan kuɗin da ake kashewa a mulki."

Kara karanta wannan
"Na kusa hakura": Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ya so ya sanya ya fasa takara a 2023
"Kudaden da aka ciyo bashi kuma da an saka su a ɓangarori masu muhimmanci."
- Peter Obi

Asali: Twitter
Bugu da ƙari, ya soki yawan kuɗin ruwa da ake karɓa a bankuna a ƙarƙashin mulkin Tinubu, yana mai cewa hakan yana hana kamfanoni yin nasara a Najeriya.
"Har ila yau, muna da ƙasa da ke fama da bashi. Wannan gwamnati ta tarar da bashin kusan Naira tiriliyan 17, amma cikin shekaru biyu, ya haura zuwa fiye da Naira tiriliyan 170."
"Kudin biyan bashi ya fi kasafin kuɗin muhimman bangarori kamar kiwon lafiya da ilimi. Kashi 70 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a ƙasar nan ba sa aiki."
"Idan da ni ne shugaban ƙasa, da na gyara asibitocinmu na matakin farko da makarantun da ke a matakin farko."
- Peter Obi
Tsohon hadimin Buhari ya caccaki Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari, ya caccaki Peter Obi kan kalaman da ya yi dangane da kisan ƴan Arewa a jihar Edo.
Bashir Ahmad ya buƙaci a tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya daina nuna ɓangaranci kan abin da ya shafi Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng