Mutuwar Galadiman Kano: Abba Ya Soke Gaisuwar Sallah a Masarautun Rano da Karaye
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhini kan rasuwar dadadden dan majalisar Sarki, Galadiman Kano, Abbas Sanusi Bayero
- Bayan rasuwar Galadiman Kano, gwamnatin jihar Kano ta soke gaisuwar karamar Sallah da masarautun Rano da Karaye aka shirya yi
- Gwamnatin Kano ta umurci jami’ai su hallara a gidan gwamnati da karfe 9:30 na safe domin tafiya jana’izar marigayin da karfe 10:00
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shiga jimami na rasuwar dadadden dan majalisar Sarki, watau Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi Bayero.
Legit Hausa ta rahoto cewa, Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, ya rasu ne a daren ranar Laraba, 2 ga watan Afrilu, 2025 bayan fama da rashin lafiya.

Asali: Facebook
Abba ya soke gaisuwar Sallah a Rano, Karaye
Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan Kano, ya fitar da sabon umarnin da Abba ya bayar kan mutuwar Alhaji Abbas a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan sanarwar rasuwar Galadiman Kano, gwamnatin jihar ta soke gaisuwar Sallah da masarautun Rano da Karaye suka shirya kai wa gwamna.
A bisa al'ada, masarautun Rano da Karaye, suna zuwa gidan gwamnatin Kano a rana ta uku bayan karamar Sallah, domin yi wa gwamna gaisuwar Sallah.
Ziyarar gaisuwar Sallar tasu na zuwa ne kwana daya bayan Sarkin Kano ya yi Hawan Nasarawa, inda yake kai wa gwamna ziyarar gaisuwar Sallah.
Umarnin gwamnatin Kano ga ma'aikata
Sanarwar Sanusi Bature ta ce:
"An soke gaisuwar Sallah a masarautun Rano da Karaye domin girmama marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi Bayero, ɗan Sarkin Kano Sanusi I, da ya rasu jiya.
"An umarci dukkanin jami’an gwamnati da su taru a fadar gwamnati da misalin karfe 9:30 na safe domin tafiya Kofar Kudu don jana’izar marigayi Galadiman Kano da za a yi da karfe 10:00 na safiyar yau.
"Ana gayyatar jama’a domin su karrama marigayi Galadiman Kano, wanda shi ne mafi dadewar mai rike sarauta a Kano.
"Allah ya jikansa da rahama, amin."
Abin da Kanawa suka ce kan umarnin Abba

Asali: Facebook
Kanawa sun yi martani da Gwamna Abba Yusuf ya soke gaisuwar Sallah a masarautar Rano da Karaye:
Muazu Mukhtar Balarabe
"Wannan abin a yaba ne, Allah ya jikansa da Rahma."
Yasa'a Hamisu:
"Allahu Akbar, Allah ya jikan dukkan Musulmai baki daya."
Muhammad Auwalu Shuaibu:
"Allah ka gafartawa bawanka Galadiman Kano, ka nuna masa Manzon Allah (SAW)."
Musa Mohammad Sani:
"Yanzun mu mutanen Abuja a ina za mu yi ta'aziyya?"
Buhari Yakubu Gajida:
"Allah ya jikan shi da rahama, Allah ya sa ya huta, Allah ya yafe mashi kura kuran shi, Allah ya sa can ta fi mashi nan."
An shiga jimamin rasuwar Galadiman Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jihar Kano ta shiga cikin alhini bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya rasu yana da shekaru 92 a daren Laraba.
Mutanen Kano sun nuna jimaminsu, suna bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi, duba da rawar da ya taka a masarautar Kano tun zamanin baya.
Asali: Legit.ng