Musulmi Sun ba Hausawa Shawara kan Kisan Gillar da Aka Yi Wa Ƴan Arewa a Edo

Musulmi Sun ba Hausawa Shawara kan Kisan Gillar da Aka Yi Wa Ƴan Arewa a Edo

  • Kungiyar musulmai (TMC) ta buƙaci jama'a musamman waɗanda kisan gillar da aka yi wa maharba a Edo ta shafa da kar su ɗauki fansa
  • TMC ta yi Allah wadai da wannan kisan gilla da aka yi wa mafarautan, tana mai cewa hakan ya kara nuna illar ɗaukar doka a hannu
  • Kungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta gudanar da bincike tare da kama duk mai hannu a wannan ɗanyen aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Wata ƙungiyar Musulmai (TMC) ta yi Allah wadai tare da alhini kan kisan gillar da aka yi wa matafiya 16 daga Arewa a garin Uromi na Jihar Edo.

Ƙungiyar TMC ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu kuma su guje wa daukar fansa.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Direba ya fadi ainihin yadda aka kashe 'yan Arewa a jihar Edo

Taswirar Edo.
Musulmi sun ba Hausawa shawara kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a kihar Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hakn na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji AbdulWasi’I Taiwo Bangbala, ya fitar ranar Talata, 1 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar musulmi ta ba mutane shawara

Ya shawarci Hausawa da sauran waɗanda aka kashe wa ƴan uwa a wannan mummunan lamarin su sa wa zukatansu ruwan sanyi, kada su ce za su ɗauki fansa.

Ya ce:

“Fada ba ya magance matsala, sai dai ya ƙara tsananta rikici da haddasa sabon fitina. Dole ne mu dogara ga shari’a da adalci domin hukunta masu laifi.”

Ya kara da cewa wannan danyen aiki da aka aikata bisa zargin da ba shi da tushe da tsautsayi, ya zama izina kan buƙatar zaman lafiya da haɗin kai a ƙasa.

TMC ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansu

Kungiyar ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tana mai cewa wannan babban rashi ne da ya jefa su cikin jimami da baƙin ciki.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala za ta maka Dan Bello a kotu kan zargin Sheikh Bala Lau

TMC ta kuma bayyana cewa wannan musiba ba wai wata matsala ce ta gari ɗaya ba, illa dai wata alama ce da ke nuna hatsarin ɗaukar doka a hannu, ƙabilanci, da kuma cin zarafin da ‘yan banga ke yi.

“Duk wani ɗan Najeriya na da haƙƙin rayuwa cikin aminci, girmamawa, da kuma adalci karkashin doka,” in ji kungiyar.
Gwamna Okpebholo.
Kungiyar musulmi sun bukaci a kwantar da hankali kan kisan ƴan Arewa a Edo Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Baya ga haka, kungiyar ta yi tir da kisan gillar da aka yi wa maharban bisa zargin aikata laifi ba tare da hujja ba, tana mai cewa hakan take doka ne kuma haɗari ga haɗin kan ƙasa.

“Kisan gilla mummunan aiki ne da ya kamata a yaƙe shi. Ko da akwai tuhuma, abin da ya dace shi ne a mika wanda ake zargi ga hukuma, ba wai a azabtar da su cikin zalunci ba.”

TMC ta bukaci a gudanar da bincike na gaskiya domin gano masu hannu a wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa irin wannan abin ba zai sake faruwa ba a nan gaba.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi matsayarsa kan umarnin hana hawan Sallah a Kano

Mutane sun fara guduwa a Uromi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mazauna garin Uromi da ke jihar Edo sun fara guduwar daga gidajen da jami'an tsaro suka fara kamen waɗanda ake zargi da kisan.

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna Uromi da kewaye sun daina zuwa gonakinsu, da yawa daga ciki sun gudu sun nemi mafaka a wasu garuruwan makwabta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262