Bikin Sallah: Limamai Sun Tsage Gaskiya ga Gwamnatin Tinubu kan Tsadar Rayuwa

Bikin Sallah: Limamai Sun Tsage Gaskiya ga Gwamnatin Tinubu kan Tsadar Rayuwa

  • Ƙungiyar limamai da malamai ta jihar Ogun ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya kan tsadar rayuwa
  • Malaman sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin tsamo mutane daga cikin halin ƙuncin da suke ciki
  • Sun kuma yi kira ga gwamnatoci a kowane matakai da su tashi tsaye domin ɗaukar matakan farfaɗo da tattalin arziƙi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Ƙungiyar limamai da malamai ta jihar Ogun ta aika saƙo ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu kan wahalar da ake sha a ƙasar nan.

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da manufofi da shirye-shirye waɗanda suka shafi jin daɗin jama’a domin rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta.

Bola Ahmed Tinubu
Malamai sun bukaci gwamnatin Tinubu ta saukakawa al'umma Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Wannan kiran na ƙunshe ne a cikin saƙon Sallah da sakataren ƙungiyar Imam Tajudeen Adewunmi Mustapha, ya sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Gwamnatin Uba Sani za ta dauki ma'aikata, ta fadi wadanda za su amfana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limamai sun jawo hankalin gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar ta bayyana cewa matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasar nan ya jefa mutane da dama cikin halin damuwa.

Ta ce saboda haka akwai buƙatar gwamnatin ta ɗauki matakan da za su kawo sauƙi ga jama'a.

"Najeriya tana fuskantar matsalolin tattalin arziƙi, rashin tsaro, hauhawar farashi da rashin kwanciyar hankali, waɗanda suka sanya rayuwa ta zama mai matuƙar wahala ga mutane da dama."
"Yanzu lokaci ne da ya kamata mu ci gaba da yin addu’a domin samun taimakon Allah (SWT) a cikin lamuranmu."
"Dole ne mu nemi Allah Ya yi wa shugabanninmu jagoranci, Ya taimaki al’ummarmu da iyalanmu, tare da yin addu’a don samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunƙasar tattalin arziƙi a ƙasarmu."
"A matsayimu na ƴan ƙasa, ya zama wajibi mu zama masu gaskiya, riƙon amanar da aka ɗora mana, da kuma aiki tuƙuru, domin bayar da gudunmuwa mai kyau ga al’ummarmu tare da tabbatar da adalci da gaskiya a cikin duk abin da muke yi.”

Kara karanta wannan

Tsadar raryuwa: Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ya samo mafita ga magidanta

“Sannan, duk da cewa muna yabawa ƙoƙarin gwamnatocin jihohi da na tarayya wajen magance wasu daga cikin matsalolin da ake fama da su, dole ne mu jaddada cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa kan wahalhalun da mutane ke fuskanta."
“Matsin tattalin arziki ya jefa mutane da dama cikin halin damuwa, don haka akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan ceto al'umma."

- Tajudeen Adewunmi Mustapha

Bola Ahmed Tinubu
Limamai sun bukaci gwamnatin Tinubu ta tausayawa talakawa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatoci a matakai daban-daban da su fifita manufofin da za su farfaɗo da tattalin arziki da kuma tabbatar da cewa kayan more rayuwa sun zama masu arha ga talakawa.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara himma wajen tabbatar da tsaron al’umma, ƙarfafa hukumomin tsaro, da tabbatar da cewa an hukunta duk waɗanda ke aikata laifuka domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.

Tinubu ya kusa haƙura da takara a 2023

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda ya kusa haƙura da yin takara a zaɓen 2023.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sauya fasalin Naira da aka yi, ya sanya gwiwoyinsa sun yi sanya kan neman shugabancin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng