Gwamnan Sokoto Ya Yi Magana da Babbar Murya kan Kisan 'Yan Arewa a Edo
- Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto ya bayyana alhininsa kan kisan wasu 'yan Arewa 16 da aka yi a Uromi, Jihar Edo
- Ahmed Aliyu Sokoto ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta kama masu hannu a kisan tare da gurfanar da su
- Bugu da kari, gwamnan ya jaddada bukatar hana tashin-tashina da tabbatar da zaman lafiya da adalci a fadin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan kisan gilla da aka yi wa wasu 'yan farauta 16 ‘yan Arewa a garin Uromi na Jihar Edo.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da gwamna Ahmed Aliyu ya yi a kan lamarin ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan danyen aikin sun fuskanci hukunci.
Yadda aka kashe 'yan Arewa a Edo
Rahotanni sun tabbatar da cewa matafiya kimanin 25 'yan asalin Arewacin Najeriya sun fito daga Fatakwal zuwa Kano sai aka tare su a garin Uromi na jihar Edo.
Biyo bayan fara bincike da 'yan banga suka yi, an bukaci mutanen su fito daga cikin motarsu baki daya.
Daga nan kuma sai aka zarge su da garkuwa da mutane, kafin bincike kuma aka fara dukansu har aka kashe 16 a cikinsu aka kona gawarsu a wajen.
Bukatar gurfanar da wadanda suka yi kisan
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa wannan harin wani babban kalubale ne da ke bukatar martani mai karfi daga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
Ya ce bai kamata irin wannan zalunci da cin zarafi ya ci gaba da faruwa ba, don haka dole ne a bi diddigin lamarin domin hukunta masu laifi.
Gwamnan ya bukaci hukumomi da su tabbatar da cewa an yi adalci, domin hana aukuwar irin wannan tashin hankalin a gaba.

Asali: Facebook
Kira ga kare rayuka da zaman lafiya
A cikin sanarwar, gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa cin zarafi da daukar doka a hannu abin Allah wadai ne a cikin al’umma mai bin doka da oda.
Ya bukaci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen hana aukuwar ire-iren wadannan hare-hare a nan gaba.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar kasa da su rungumi zaman lafiya da mutunta juna domin samar da ingantacciyar rayuwa da ci gaban kasa.
Yanzu dai ana jiran matakan da hukumomi za su dauka kan wannan mummunan lamari, tare da fatan ganin an yi adalci domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

Kara karanta wannan
Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo
Musawa ta yi magana kan kisan Edo
A wani rahoton, kun ji cewa ministar al'adun Najeriya Hannatu Musa Musawa ta yi Allah wadai da kisan Hausawa a jihar Edo.
Ministar ta yi kira ga hukumomi su tabbatar da cewa an kama wadanda suka yi laifin tare da hukunta su domin hakan ya zama izina ga wasu a gaba.
Asali: Legit.ng