Biyan Diyya da Alkawuran da Abba Kabir Ya Yi kan Hausawan da aka Kashe a Edo
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya taya al’ummar Musulmi murnar sallar azumi tare da kira ga hadin kai da tausayin juna
- Abba Kabir ya nuna alhini kan kisan da aka yi wa ‘yan asalin Kano a Edo, yana mai cewa za su tabbatar an gurfanar da masu laifin
- Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an biya diyyar mutanen tare da kwato duk wani hakki na su ko na iyalansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika da sakon taya murna ga daukacin Musulmi a Kano da kewayenta yayin da suke bikin sallar azumi.
Ya kuma bukaci al’ummar Kano da su tallafa wa mabukata da kuma kokarin samar da zaman lafiya a cikin al’ummominsu domin ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

Asali: Facebook
A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook, gwamnan ya bayyana matakin da suke dauka kan Hausawan da aka kashe a Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Kabir ya bukaci Musulmi su ci gaba da rayuwa bisa hakuri, tausayi da hadin kai, kamar yadda suka yi a watan Ramadan.
Alhini kan kisan Hausawa a Edo
Da yake magana kan kisan da aka yi wa wasu ‘yan asalin Kano a Jihar Edo, Abba Kabir Yusuf ya bayyana matukar bakin ciki kan mummunan lamarin.
Ya tabbatar wa da al’ummar Kano cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su gaban shari’a.
Maganar biyan diyya da tura tawaga Edo
Abba Kabir Yusuf ya ce ya hada tawaga ta musamman da za ta tashi daga Kano har zuwa Edo domin tattaunawa da Hausawan jihar da kuma gwamnan jihar kan lamarin.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
A bidiyon da ya wallafa a Facebook, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an biya diyyar mutanen da aka kashe.
Haka zalika ya bayyana cewa gwamnan Edo ya kira shi a waya kan lamarin, kuma ya tabbatar masa da cewa ana daukar matakin kama masu laifin.
Gwamnan ya ce an kama mutane da dama kuma za a tafi da su Abuja domin bincike da daukar matakin da ya dace.

Asali: Facebook
Kira ga zaman lafiya da girmama juna
Abba Kabir Yusuf ya bukaci al’ummar Kano da su yi amfani da wannan lokaci na Idi domin karfafa dangantaka, yin sulhu da juna da kuma kokarin samar da zaman lafiya.
Ya kuma yi kira da a yi koyi da halayen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta hanyar rikon gaskiya, adalci da tausayi a dukkan al’amura.
Maganar Abba kan cigaban Kano
Abba Kabir ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kokarin kyautata rayuwar jama’a ta fuskar habaka tattalin arziki, walwala da samar da abubuwan more rayuwa.
Ya bayyana cewa hadin kai da zaman lafiya tsakanin kabilu da addinai daban-daban shi ne abin da ke kara daukakar Kano.
Haka kuma ya bukaci ‘yan jihar da su ci gaba da yin aiki tukuru domin samun ci gaba da zaman lafiya mai dorewa a jihar Kano da kasa baki daya.
An kama wadanda suka kashe Hausawa a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa an kama mutane 14 cikin wadanda ake zargi da kisan Hausawa a jihar Edo.
Rundunar 'yan sanda ta kasa ne ta tabbatar da hakan tare da yin kira ga al'umma da su kaucewa daukar doka a hannu idan aka samu irin haka.
Asali: Legit.ng