Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ya Ki Daukar Shawara, Ya Nada Mai Sukarsa Minista

Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ya Ki Daukar Shawara, Ya Nada Mai Sukarsa Minista

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da ya ɗauka na naɗa Bosun Tijani a muƙamin ministan sadarwa
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa naɗin da ya yi wa Bosun Tijani ya kasance abu ne mai wahala saboda na kusa da shi ba su so ba
  • Tinubu ya nuna cewa duk da Bosun ya kasance mai sukarsa a baya, hakan ba zai hana a jawo shi ya zo ya ba da irin ta sa gudunmawar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan naɗa Bosun Tijani muƙamin ministan duk da irin sukar da ya yi masa a baya.

Shugaba Tinubu ya ce shawarar da ya yanke na naɗa Dr. Bosun Tijani a matsayin ministan sadarwa, hujja ce da ke nuna cewa yana girmama mutane masu basira.

Kara karanta wannan

"Na kusa hakura": Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ya so ya sanya ya fasa takara a 2023

Bola Ahmed Tinubu
Tinubu ya fadi dalilin nada Bosun Tijani mukamin minista Hoto: @bosuntijani, @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a daren ranar Asabar a wajen wats liyafar buɗa baki ta musamman da aka shirya a fadar shugaban ƙasa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bosun Tijani na cikin manyan baƙi da suka gabatar da saƙonnin fatan alheri ga Shugaba Tinubu, tare da mataimakin shugaban lasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da sauran manyan baƙi.

Bosun Tijani ya yi mamakin samun minista

A jawabinsa, Bosun Tijani ya yi bayanin yadda Shugaba Tinubu ya naɗa shi minista duk da cewa a baya ya kasance mai fafutuka kuma yana sukar shugaban ƙasa da majalisar tarayya.

"Kafin a naɗa ni, ban taɓa haɗuwa da shugaban ƙasa ba. Amma bayan an tabbatar da ni, ya ce min, ‘Na duba tarihin aikinka da fafutukarka, kuma na ga cewa akwai wani abu a tare da kai. Na ba ka wannan dama don ka wakilci ƙasarka ka kuma taimaka wajen inganta ta."

Kara karanta wannan

Shekara 73: Buhari ga aika sako ga Tinubu, ya fadi yadda dangantakarsu ta ke

"Na yi tunanin za a yi min gagarumar suka saboda tarihin da nake da shi, amma irin fahimtar da na gani a wajen shugaban ƙasa, wani abu ne da na taɓa fuskanta a karon farko a rayuwata."
"Na tuna cewa a wannan taro, wasu sun sake fito da tarihin abubuwan da na yi, suna cewa, ya faɗi wannan, ya aikata wannan.’ Amma Shugaban Ƙasa ya ce, ‘A yi shiru!’"

- Bosun Tijani

Bosun Tijani
Bosun Tijani ya ce Tinubu ya ba shi mamaki Hoto: @bosuntijani
Asali: Twitter

Meyasa Tinubu ya ba mai sukarsa minista?

Yayin da yake mayar da martani ga bayanan ministan, Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa naɗa Bosun Tijani a matsayin minista ya kasance abu mai wahala, ganin irin ƙorafin da makusantan shi suka yi.

"Lokacin da na zaɓe shi, abu ne mai wahala. Wasu daga cikin aminaina na kusa, waɗanda suka karanta maganganunsa a shafukan sada zumunta, sun zo suka ce, ‘A’a, ba za ta yiwu ba.’"
"Na ce, ‘Eh, yana da basira. Saboda yana suka ta kuma yana zagin majalisa, hakan ba yana nufin ba shi da gudunmawar da zai bayar ba."

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi maganar kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo

"Wataƙila fushinsa a wancan lokaci zai ƙarfafa shi ya ba da gudunmawa sosai ga harkokin mulki. Kuma a yau, yana yin hakan, kuma ina alfahari da shi."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya kusa haƙura da takara a 2023

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya kusa haƙura ya janye daga yin takara a 2023.

Shugaba Tinubu ya nuna cewa ya kusa fasa takarar ne saboda yadda tsarin sauya fasalin kuɗin Naira ya jawo tarin matsaloli a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel