Bikin Sallah: Ganduje Ya Tura Sako Mai Muhimmanci ga Musulmi bayan Kammala Azumi
- Abdullahi Umar Ganduje ya aika da sakon taya murna ga al'ummar Musulmi na kammala azumin watan Ramadan
- Shugaban na jam'iyyar APC na ƙasa, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da nuna halin tausayi musamman ga marasa galihu a cikin al'umma
- Gandujw ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu'a domin ya samu nasara a mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ta ya al'ummar Musulmi murnar zuwan lokacin ƙaramar Sallah.
Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da nuna soyayya da tausayi ga juna, musamman ga marasa galihu a cikin al’umma.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Edwin Olofu, babban sakataren ƴaɗa labarai na Ganduje, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukukuwan ƙaramar Sallah suna nuna ƙarshen azumin Ramadan, wanda yana ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci.
Ganduje ya taya Musulmi murnar zuwan Sallah
Ganduje ya taya al'ummar Musulmi murnar komawa ga Allah da gudanar da ibada a cikin wata mai alfarma na Ramadan.
Shugaban na APC ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da riƙe halayen tsoron Allah, sadaukarwa, da jinƙai da watan Ramadan ke koyarwa.
"Yayin da Najeriya ke ci gaba da tafiya a kan hanyar bunƙasa da ci gaba, shugaban APC na ƙasa ya yi kira ga Musulmi da duk ƴan ƙasa da su kasance masu ɗa’a wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, da cigaban ƙasa."
"Ya jaddada cewa darussan watan Ramadan na haƙuri, sadaukarwa, da juriya su ne tubalin da za su taimaka wajen samar da daidaito da ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar nan."
"Tsohon gwamnan na Kano ya buƙaci al’ummar Musulmi da ƴan Najeriya da su yi addu’a ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don ya samu nasarar fitar da ƙasar nan daga matsalolin tattalin arziƙi da kuma kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da ake fuskanta."
"Ganduje ya jaddada cewa ƴan Najeriya ba za su yi nadamar zaɓen Tinubu ba bayan ya kammala wa’adinsa na farko."

Asali: Facebook
“Dr. Ganduje ya kuma yabawa ƴan Najeriya bisa cikakken goyon bayan da suke bai wa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin APC na da niyyar inganta walwala da jin daɗin duk ƴan ƙasa."
"A ƙarshe, Shugaban APC na ƙasa ya miƙa fatan alheri da addu’ar cewa Allah (SWT) ya amshi addu’o’i da sadaukarwar al’ummar Musulmi, ya kuma albarkace su da rahama da ni’ima a wannan lokaci na shagulgula."
- Edwin Olofu
Sanusi II ga goyi bayan hana Hawan Sallah
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi IO ya goyi bayan matakin da jami'an ƴan sanda suka ɗauka na hana hawan Sallah a Kano.
Sanusi II ya bayyana cewa shi a wurinsa bai ɗauki hawan Sallah a matsayin abun a mutu ko a yi rai ba, inda ya buƙaci mutane da su kwantar da hankulansu.
Asali: Legit.ng