"Na Kusa Hakura": Tinubu Ya Fadi Abu 1 da Ya So Ya Sanya Ya Fasa Takara a 2023
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tuna baya kan yadda ya kusa haƙura da burinsa na yi takara a zaɓen 2023
- Mai girma Bola Tinubu ya nuna cewa ya kusa janyewa daga yin takara saboda yadda sauya fasalin Naira ya dagula al'amura a ƙasar nan
- Sai dai, shugaban ƙasan ya bayyana cewa ƙwarin gwiwar da ya samu daga na kusa da shi, ya sanya ya yi takarar kuma har ya samu nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana yadda ya kusa haƙura ɗa yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa matsalar tattalin arziki da ta addabi Najeriya sakamakon sauya fasalin Naira, ta kusa sanyawa ya janye daga takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.

Asali: Facebook
Hadimin Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya shirya buɗa baki tare da manyan ƙasa
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen buɗa baki na musamman da aka shirya a fadar gwamnati da ke Abuja.
Shugaban ƙasan ya tuna yadda wata tattaunawa da wani ɗan uwansa mai kusanci da shi, ta kusan sanyawa ya sake tunani kan burinsa na yin takara.
Buɗa bakin ya zo daidai da zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekara 73 a duniya, kuma ya yi amfani da damar wajen nuna godiya ga ƴan Najeriya bisa irin addu’o’i da fatan alheri da suka yi masa.
Mutanen da ke wurin buɗa bakin sun haɗa da uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da matarsa Nana Shettima, mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da shugabannin majalisar dokoki ta tarayya.
Sauran sun haɗa gwamnoni na yanzu da tsofaffi, jakadu, manyan ƴan kasuwa, shugabannin addini, da wasu daga cikin abokanan Shugaba Tinubu na tun yarinta.

Kara karanta wannan
"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027
Yadda Tinubu ya kusa haƙura da yin takara
Yayin da yake tunawa da ƙalubalen da ya fuskanta a zaɓen 2023, Tinubu ya bayyana yadda wata tattaunawa da wani ɗan uwansa ta sa ya yi tunanin janyewa daga takarar.
"Mutanen da ke kusa da ni sun san cewa abubuwa ba su tafiya min daidai. A lokacin yaƙin neman zaɓe, wani daga cikinsu ya zo falo na da misalin ƙarfe 3:30 na dare, ya ce min yana buƙatar N50,000 don ya siyowa kawunmu kayan abinci."
"Ya ce min, 'babu kuɗaɗe saboda kai'. Mutane suna zuwa daga wannan bankin zuwa wannan saboda babu kuɗi. Kawunmu, wanda attajiri ne, bai da tsabar kuɗi N10,000 a hannunsa. Takarar me zaka yi'?"
"Na ce masa, ‘Ina takarar shugabancin ƙasa ne, ba don kai da kawu ba.’ Na ba shi N50,000. Yayin da yake fita, ya juyo ya ce min, ‘Ba na tunanin cewa za ka yi nasara.’ Na amsa da cewa, ‘Zan yi nasara."

Kara karanta wannan
Atiku ya tuna baya, ya fadi dalilin kin zabar Wike a matsayin mataimakinsa a 2023
- Shugaba Bola Tinubu

Asali: Twitter
Shugaban Kasar ya ce daga baya kawunsa ya kira shi don tabbatar masa da samun kuɗin, amma ya bayyana cewa ya ba wanda aka aiko N10,000 ne kawai, sannan ya riƙe sauran.
"Na yi mamaki. A lokacin, na kusan janye batun takara. Amma godiya ta tabbata ga Aminu Masari da duk wanda suka ƙarfafa min gwiwa. Da na zo Abuja, Masari ya ce min, ‘Ni ne shugaban ƙungiyar Arewa maso Yamma; kar ka karaya.’"
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ya karɓi mulki a lokacin da tattalin arziƙin ƙasar nan ke cikin mawuyacin hali, kuma dole ne ya ɗauki matakai masu tsauri da suka haɗa da cire tallafin mai.
Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara 73
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya mai girma Bola Tinubu murnar cika shekara 73 a duniya.
Buhari ya yi addu'ar samun tsawon kwana da lafiya ga shugaban ƙasan na Najeriya wanda ya gaje shi a kan mulki.
Asali: Legit.ng