Ministar Al'adun Najeriya Ta Yi Kakkausar Magana kan Kisan Hausawa a Edo

Ministar Al'adun Najeriya Ta Yi Kakkausar Magana kan Kisan Hausawa a Edo

  • Ministar Al’adu, Hannatu Musa Musawa, ta nuna matukar bakin ciki kan kisan da aka yi wa wasu matafiya 'yan Arewa a Edo
  • Hannatu Musawa ta yabawa Gwamna Monday Okpebholo bisa yadda ya yi tir da lamarin tare da bada umarnin g udanar da bincike
  • Ta kuma bukaci a kamo duk masu hannu a lamarin tare da hukunta su domin hana yawaitar daukar doka a hannu a gaba

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministar Al’adun Najeriya, Hannatu Musa Musawa, ta bayyana kisan wasu matafiya 'yan Arewa da aka yi a Edo a matsayin abin takaici da rashin imani.

A cewarta, wannan lamari da ya faru a Uromi ya nuna cewa har yanzu akwai matsalar daukar doka a hannu a wasu yankuna na kasar nan.

Musawa
Hannatu Musawa ta yi Allah wadai da kisan Hausawa a Edo. Hoto: @hanneymusawa
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan abin da Hannatu Musa Musawa ta yi ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sakon, ministar ta bukaci a gaggauta hukunta duk masu hannu a lamarin domin ya zama izina ga wasu masu niyyar aikata irin hakan.

Minista ta yaba da matakin gwamnan Edo

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Hannatu Musa Musawa ta jinjinawa Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo, bisa yadda ya yi Allah wadai da kisan gillar.

Ta ce matakin da gwamnan ya dauka na bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin ya nuna kishinsa ga tabbatar da adalci.

A cewar ta:

" Dole ne na yaba wa gwamna Monday Okpebholo a kan yadda ya yi Allah wadai da kisan gillar tare da kaddamar da cikakken bincike."

Wasu matasa ne suka kashe Hausawa suna dawowa gida daga f arauta kuma suka suka kona gawarsu a jihar Edo.

Gwamnan Edo
Gwamnan Edo ya yi Allah wadai da kisan Hausawa a jiharsa. Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Bukatar a hukunta wadanda ke da laifi

Kara karanta wannan

An fara kama mutanen da suka kashe 'yan Arewa a Edo

Ministar ta bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi a wannan aika-aika ya fuskanci hukunci.

Ta yi nuni da cewa idan ba a dauki matakin doka ba, irin wannan ta’asa na iya ci gaba da faruwa a nan gaba.

A cewar ta:

" Ya kamata wannan lamarin ya zama izina ga kowa.
Duk wanda aka samu da hannu a wannan kisan dole ne ya fuskanci hukunci domin hana yawaitar irin wannan aika-aika a nan gaba."

Ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe

Hannatu Musa Musawa ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan hari.

Ta bayyana cewa tana tare da su a cikin wannan lokaci na jimami tare da addu’ar Allah ya jikan mamatan.

Yanzu haka dai ana sa ido don ganin yadda hukumomi za su tafiyar da bincike da kuma matakin da za a dauka domin tabbatar da adalci.

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

An kama wasu da suka kashe Hausawa a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta fara daukar mataki kan wadanda suka kashe Hausawa a jihar Edo.

Rahotanni sun nuna cewa sufeton 'yan sanda ya tabbatar da cewa an kama mutane 14 yayin da ake cigaba da kokarin cafke sauran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng