An Kona 'Yan Arewa Kurmus Suna Dawowa Gida Hutun Sallah a Jihar Edo

An Kona 'Yan Arewa Kurmus Suna Dawowa Gida Hutun Sallah a Jihar Edo

  • An kashe wasu matafiya 16 daga Arewacin Najeriya sakamakon zargi maras tushe da aka yi musu a jihar Edo
  • ‘Yan sa-kai sun zarge su da laifin garkuwa da mutane, lamarin da ya haddasa kashe su ba tare da bincike ba
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Wani mummunan lamari ya faru a Udune Efandion, yankin Uromi a Jihar Edo, aka kashe mutane 16 ‘yan asalin Arewacin Najeriya bisa zargi maras tushe.

Matafiyan, galibi farautar daji suke yi a yankinsu, suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano domin bikin Sallah a ranar Alhamis lokacin da ‘yan sa-kai suka tare su.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya sanar da rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Baba Karkuzu

Arewa
An kashe yan Arewa suna dawowa gida a Edo. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an kama wasu daga cikin wandanda ake zargi da aikata mugun aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyoyi, an zargi matafiyan da garkuwa da mutane bisa ganin makaman farauta da suke dauke da su, wanda hakan ya haddasa tashin hankali da harin da ya kai ga mutuwarsu.

Yadda aka kashe 'yan Arewa a Edo

Rahotanni sun nuna cewa da misalin karfe 1:30 na rana, Edo State Security Corps tare da wasu ‘yan sa-kai suka tare motocin matafiyan, suka zarge su da kasancewa masu garkuwa.

Ba tare da bincike ba, sai suka dauki matakin kira ga matasa, wanda ya haddasa farmaki kan matafiyan.

A cikin kankanin lokaci, wasu fusatattun matasa suka fara dukan mutafiyan, suka banka wa motocinsu wuta da wasu daga cikin gawarwakinsu.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka kashe an jefar da su cikin wuta, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici da takaici.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

‘Yan sanda sun kama mutane 5

A lokacin da dakarun tsaro suka isa wurin, mai aukuwa ta auku, aka samu mutane hudu da suka tsira da ransu, aka garzaya da su asibiti.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama mutum biyar da ake zargi da hannu a lamarin, tare da alkawarin tabbatar da cewa doka za ta yi aikinta.

Duk da haka, ‘yan uwa da al’ummar da lamarin ya shafa na kokwanto kan ko hakikanin masu laifin za su fuskanci hukunci mai tsanani.

Yan sanda
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Bukatar adalci da kare hakkin jama’a

Bayan aukuwar wannan hari, al’ummar Hausawa a Uromi sun yi zaman gaggawa domin tattauna hanyoyin da za a hana afkuwar irin haka a gaba.

Wasu kungiyoyi da masu fashin baki sun bukaci a dauki matakin doka kan duk wadanda suka aikata wannan ta’asa.

A cewar su, irin wannan danyen aiki yana haifar da rashin zaman lafiya da rura wutar gaba tsakanin kabilu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Fubara ya magantu kan fasa bututun mai a Ribas, ya fadi gaskiyar me ke faruwa

An kashe Kachalla Isuhu a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun Najeriya sun yi nasarar hallaka dan ta'adda, Kachalla Isuhu a jihar Zamfara a ranar 27 ga watan Maris 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Kachalla Isuhu ya shahara da ta'addanci wajen saka wa kauyuka haraji, kuma shi ya kashe Farfesa Yusuf Sa'idu na jamai'ar Danfodiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng