Tinubu Ya Kadu kan Rasuwar Mahaifiyar Gwamna Radda, Ya Tura Sako Mai Muhimmanci

Tinubu Ya Kadu kan Rasuwar Mahaifiyar Gwamna Radda, Ya Tura Sako Mai Muhimmanci

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar mahaifiyar gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda
  • Mai girma Bola Tinubu ya yi wa Gwamna Radda ta'aziyya kan rasuwar Hajiya Safara'u Umaru Baribari wacce ta rasu tana da shekara 93 a duniya
  • Ya bayyana marigayiyar a matsayin wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen gina al'umma da taimaka musu
  • Shugaba Tinubu ya yi addu'ar Allah Ya ji kanta Ya kuma sanya ta a cikin Aljannatul Firdausi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari.

Marigayiyar, wacce ta rasu tana da shekaru 93 a duniya, ta riga mu gidan gaskiya a daren Asabar, 23 ga watan Maris 2025 a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Duniya ba tabbas: Mahaifiyar Gwamna Dikko Radda ta rasu ana azumin Ramadan

Tinubu ya yi wa Gwamna Radda ta'aziyya
Tinubu ya yi wa Gwamna Radda ta'aziyya kan rasuwar mahaifiyarsa Hoto: @DOlusegun, @dikko_radda
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Radda

Shugaba Tinubu ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin mace tagari wacce ta tarbiyyantar da shugabanni da dama, waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban.

Ya jaddada cewa rayuwarta ta kasance mai cike da gaskiya da kishin al’umma, inda mutane da dama suka yi koyi da waɗannan halayen na ta masu kyau, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Shugaban ƙasan ya yi addu’ar Allah Ya jikanta, Ya sanya ta cikin Aljannar Firdausi, tare da roƙon Allah Ya bai wa iyalanta ƙwarin gwiwar jure wannan rashin da aka yi musu.

"Shugaba Bola Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari."

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi damuwarsu kan dokar ta ɓaci a Ribas, sun ambaci Kano

"Marigayiyar mai shekaru 93 a duniya ta rasu a daren ranar Asabar."
"Shugaba Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai sadaukarwa, wacce ta reni shugabanni da dama da suka yi fice a fannoni daban-daban."
"Shugaban ƙasan ya ce Hajiya Safara’u ta bar tarihi mai ɗimbin daraja na gaskiya da hidima ga al’umma, wanda ya shiga lungu da saƙo."
"Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya sanya ta cikin Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalanta juriya a wannan lokaci na baƙin ciki."

- Bayo Onanuga

SERAP ta maka Tinubu ƙara a gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta ɗauki matakin shari'a kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu saboda dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar Rivers.

SERAP a cikin ƙarar da ta shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayyana dakatarwar da shugaban ƙasan ya yi musu a matsayin abin ds ya saɓa ƙa'ida.

Ta buƙaci kotun da ta shugaban riƙon da Bola Tinubu ya naɗa ci gaba da jan ragamar jihar mai arziƙin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel