El Rufai Ya Tono Yadda Ake Ruf da Ciki da Kudin Kaduna a Mulkin Uba Sani
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ci gaba da zarge-zarge kan gwamnatin Uba Sani
- El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani na ruf da ciki da kuɗaɗen Kaduna, musamman na ƙananan hukumomi
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa suna sane da yadda ake karkatar da kuɗaɗen jihar Kaduna domin siyan gidaje a ƙasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi sabon zargi kan gwamnatin Uba Sani.
Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani tana yin ruf da ciki da kuɗaɗen jihar Kaduna.

Asali: Twitter
Tsohon gwamnan ya yi wannan zargin ne yayin wata tattaunawa da Freedom Rediyo Kaduna wacce aka sanya a shafin Youtube.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Uba Sani
El-Rufai ya yi zargin cewa ana yin sama da faɗi da kuɗin ƙananan hukumomi a gwamnatin Uba Sani.

Kara karanta wannan
"40% ake ba shi," El Rufai ya zargi Uba Sani da yin kashe mu raba da ƴan kwangila
Ya nuna cewa ana ruf da ciki da kuɗin ne domin siyan gidaje a ƙasashen waje
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk abin da gwamnatin Uba Sani ke yi na ruf da ciki da kuɗi, a tafin hannunsu suke domin suna sane da komai.
"Dole ne mu fito da abin da suke yi, sun ɗauka ba mu sani ba, kuma Wallahi mun san komai. Yadda ake ruf da ciki da kuɗin ƙananan hukumomi, mun sani muna da dukkanin bayanan."
"Lokacin da na ke Kaduna ba wata ƙaramar hukuma da za ta ce muna ɗaukar sisinsu, ba ma yi, kuɗinsu muke ba su, su yi aikinsu."
"Kuɗinsu muke ba su, ba mu taɓa kuɗinsu. Suna nan ciyamomin suna da rai, ƴan APC da ƴan PDP duk su faɗa."
"Amma a yanzu babu ƙaramar hukumar da take samun N50m a wata. Domin wuf ake yi da kuɗin aje a siya daloli, ana siyan gidaje a Seychelles, ana siyan gidaje a Afrika ta Kudu, Landan da wurare da dama."
"Abin da suke yi kenan kuma duk mun sani. Mun yi shiru muna kallonsu. Amma kasan idan ka yi shiru sai a ɗauka ko tsoro kake ji, ko kai shashasha ne ba ka sani ba."
"Mun san komai, da inda ake fitar da kuɗin daga gwamnati, da wurin masu canji da ake siyan abin nan, komai mun sani."
"Su da suke cewa wane ya yi kaza wane ya yi kaza, su ne suke yi, kuma abin da suke yi ninkin ba ninkin na abin da suke zargin wasu na yi ne."
- Nasir Ahmad El-Rufai
El-Rufai ya caccaki ƴan majalisar Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi Allah wadai da ƴan majalisar dokokin jihar kan binciken da suke yi wa gwamnatinsa.
El-Rufai ya musanta karkatar da kuɗin gwamnati, a nan aka ji cewa cewa ko kaɗan baya tsoron shari'a domin ya kare kansa.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa gaba ɗaya ƴan majalisar ba su da ilmin da za su gudanar bincike na ƙwarai a kansa ko gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng