Araha Kamar Gidan Biki: Gwamnatin Sokoto Ta Dauki Matakin Karya Farashin Kayan Abinci
- Gwamnatin jihar Sokoto na son al'umma su samu kayan abinci a farashi mai rahusa musamman a watan azumin Ramadan
- A bisa hakan, gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Ahmed Aliyu ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya da ƙungiyar dillalan kayayyakin abinci
- A ƙarƙashin yarjejeniyar, za a riƙa samar da kayan abinci da sauran kayan masarufi a kan farashi mai rahusa ga jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmad Aliyu, ta ɗauki matakin rage farashin kayan abinci.
Gwamnatin ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar dillalan kayayyaki domin ganin an rage farashin.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Sokoto za ta karya farashin abinci
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manyan matakan da take ɗauka domin sauƙaƙa wahalhalun da jama’a ke fuskanta.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya
A cewar gwamnan, gwamnatin jihar ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ne da dillalan domin ganin an sauke farashin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki.
A ƙarƙashin shirin, gwamnatin za ta riƙa ba da tallafin kuɗi ga dillalan domin rage musu kuɗin da suke kashewa wajen samar da kayayyakin.
Shirin zai taimaka wajen sauƙaƙa rayuwa ga al’umma musamman a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda da yawa daga cikin jama’a na fuskantar matsalolin tsadar kayan abinci
Wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen saukaka waɗannan matsaloli ta hanyar rage farashin kayan masarufi.
Shirin zai amfani talakawa da masu ƙaramin karfi, wadanda ke fama da matsin tattalin arziƙi.
Da wannan mataki, jama’a za su iya siyan abinci da sauran kayayyakin buƙata ba tare da wahala ba.
Wane mataki gwamnatin ta ɗauka?
"A wani mataki mai cike da tarihi don rage wahalhalun da al’ummarmu ke fuskanta, musamman a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan."
"Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙulla wata gagarumar yarjejeniya da ƙungiyar dillalan kayayyaki domin rage farashin abinci da muhimman kayayyaki a faɗin jihar."
"Ta hanyar wannan haɗin gwiwa, muna samar da tallafin kuɗi domin rage tsadar kaya da tabbatar da cewa jama’a za su iya samun su a farashi mai sauƙi."
"Wannan mataki yana kara tabbatar da jajircewarmu wajen inganta jin daɗin al’umma da bunƙasa tattalin arziƙi.
"Muna fatan wannan yunƙuri zai kawo sauƙi da albarka ga kowa."
- Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto
Gwamnati ta taimaka sosai
Wani mazaunin birnin Sokoto, Dalhat Usman, ya shaidawa Legit Hausa cewa matakin da gwamnatin ta ɗauka abin a yaba ne.
"Tabbas wannan abin yabawa ne domin za a taimakawa mutane sosai, wajen samun sauƙin rayuwa.
"Muna godiya sosai domin haƙiƙa mutane za su amfana da shirin."
- Dalhat Usman
Gwamnatin Sokoto ta faɗaɗa shirin ciyarwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauki matakin faɗaɗa shirin ciyarwa a lokacin azumin watan Ramadan.
Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya ware N1.55bn domin rabawa ga wuraren da ake ba da abincin watan Ramadan a faɗin ƙananan hukumomin jihar.
A ƙarƙashin shirin, kowace gunduma daga cikin gundumomi 244 za ta samu N 5m domin raba abinci ga mabuƙata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng