Takaddamar Akpabio da Natasha: Zanga Zanga Ta Barke a Majalisa, An Samu Bayanai
- Magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sun gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar tarayya da ke birnin Abuja
- Masu zanga-zangar waɗanda suka haɗa da mata da maza sun buƙaci shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya bar muƙaminsa
- Sun kuma buƙaci kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa da ya fasa binciken zargin rashin ɗa'a da ake yi wa Sanata Natasha
- Jami'an ƴan sanda da ke majalisar a Abuja sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba musu hayaƙi mai sa hawaye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Masu zanga-zanga da ke goyon bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sun mamaye ƙofar majalisar tarayya a ranar Laraba.
Masu zanga-zangar sun fito ne kan zargin cin zarafi da ake yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce masu zanga-zangar, da suka haɗa da mata da maza daga yankin mazaɓar Kogi ta Tsakiya, suna ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin lauyoyin Sanata Natasha, Victor Giwa.
Me masu zanga-zangar suke so a yi?
Masu zanga-zangar sun riƙe kwalaye, tutoci, da alluna waɗanda suke ɗauke da saƙonni daban-daban.
Sun buƙaci kwamitin ladabtarwa da karɓar ƙorafe-ƙorafe na majalisar dattawa, wanda aka turawa binciken zargin rashin ɗa'ar Sanata Natasha da ya janye daga bincikarta.
A cewarsu, ba zai yiwu mutum ya zama alƙalin da zai yanke hukunci a kansa ba.
Sun buƙaci Sanata Godswill Akpabio da ya sauka daga muƙaminsa domin ba da dama a gudanar da binciken ba tare da nuna son zuciya ba.
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, Victor Giwa ya bayyana cewa ofishin lauyoyinsu ya samu umarnin kotu da ke dakatar da kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa daga ci gaba da binciken.
Ya ce ba za a iya sa ran cewa shugaban kwamitin da mambobinsa za su yanke hukunci cikin adalci ba, kasancewar Akpabio ne ya naɗa su.
Ƴan sanda sun kori masu zanga-zanga

Kara karanta wannan
Zargin 'neman lalata' ya ƙara girma, Sanata Natasha ta gabatar da takarda a Majalisa
Jaridar TheCable ta rahoto cewa jami’an ƴan sanda sun fatattaki masu zanga-zangar.
Ƴan sandan sun harba hayaƙi mai sa hawaye domin hana magoya bayan Natasha Akpoti-Uduaghan shiga cikin harabar majalisar tarayyar.
Masu zanga-zangar dai sun fito ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe kafin a fara zaman majalisar na ranar Laraba.
Sai dai, jami’an tsaron ba su yi wata-wata ba suka ci gaba da tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba musu hayaki mai sa hawaye.
Daga nan ne sai dandazon masu zanga-zangar su ka koma dandalin Unity Fountain.
Mutanen da Natasha ta zarga da ci mata zarafi
A wani labarin kuma, mun kawo muku manyan mutanen da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta taɓa zarga da ci mata zarafi.
Na baya-bayan nan daga cikinsu shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio wanda ya fito daga jihar Akwa Ibom.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
