Kudirin Kirkiro Karin Jiha 1 a Najeriya Ya Samu Goyon Baya, Sanata Kalu Ya Jero Dalilai

Kudirin Kirkiro Karin Jiha 1 a Najeriya Ya Samu Goyon Baya, Sanata Kalu Ya Jero Dalilai

  • Orji Uzor Kalu ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kudirin kirkiro Anioma domin ta zama jiha ta shida a Kudu maso Gabas
  • Sanata Kalu ya ce akwai bukatar kirkiro wannan jiha domin cire tunanin da Ibo ke yi cewa ana nuna masu wariya a Najeriya
  • Tun farko Sanata Ned Nwoko na Delta ya goyi bayan kirkiro jihar Anioma wadda ya ce za ta gyara kuskuren da aka yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana goyon bayansa ga kirkiro jihar Anioma a Najeriya.

Sanata Kalu ya ce ƙirƙiro jihar Anioma daga cikin jihar Delta zai cike gurbin da ke akwai a yankin Kudu Maso Gabas.

Sanata Orji Kalu.
Sanata Orji Kalu ya goyi bayan kara jiha 1 a Kudu maso Gabas Hoto: @OUKTweets
Source: Twitter

Orji Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na tashar Channels TV.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta tsallaka, ta kai harin ramuwar gayya a Neja, ta kashe bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu, Kudu maso Gabas ita ce yankin da ke da mafi ƙarancin jihohi a Najeriya da jihohi biyar kacal, sabanin wasu yankuna da ke da shida ko fiye.

Sanata Kalu, ya ce kirkiro jihar Anioma zai taimaka wajen magance tunanin da ƴan ƙabilar Igbo watau inyamurai ke yi cewa ana nuna masu wariya a Najeriya.

Kalu: "Ya kamata a samar da jihar Anioma"

A cewarsa:

"Tabbas, ya kamata a kirkiro jihar Anioma a matsayin jiha ta shida a Kudu Maso Gabas. Ita ce kawai jihar da za ta iya zama mai inganci idan an kirkiro ta."

Sanatan ya jaddada cewa mutanen Anioma inyamurai ne kuma su kansu ba su taɓa musanta hakan ba.

"Saboda haka, jihar da za a ƙirƙira don cike giɓin Kudu Maso Gabas, dole ne ta fito daga Anioma," in ji Kalu.

Sanata Ned Nwoko ya goyi bayan jihar Anioma

Tun da fari, Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa, ya nemi kirkiro wannan jiha da nufin gyara kuskuren da aka yi na rashin baKudu Maso Gabas jiha ta shida.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Sanata Nwoko ya bayyana cewa rashin daidaiton yawan jihohi a Najeriya na jawo matsala wajen wakilci da rabon albarkatun ƙasa, Leadership ta kawo.

Kudu maso Gabas tana da ‘yan majalisa 15 a Majalisar Dattawa, yayin da sauran yankuna (ban da Arewa Maso Yamma da ke da jihohi 7) ke da 18.

Majalisa ta yi fatali da kirƙiro jihohi 31

Duk da irin waɗannan buƙatu, a kwanakin baya kwamitin Majalisar Wakilai ya ƙi amincewa da kudirorin kirkiro sababbin jihohi 31.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar wakilai ya ce bukatun ƙirkiro sababbin jihohin ba su cika sharuɗɗan kundin tsarin mulki ba.

Duk da cewa ana ci gaba da samun matsin lamba daga shuwagabannin Kudu Maso Gabas, har yanzu babu wata jiha da aka amince za a kirkiro a Najeriya.

Barau ya goyi bayan jihar Karaɗuwa

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Barau Jibrin ya goyi bayan kudirin kirkiro jihar Karaɗuwa a Arewa maso Yamma.

Sanata Barau Jibrin ya ce zai yi aiki tare da Sanata Muntari Dan-Dutse, mai wakiltar Funtua a majalisar dattawa, domin ganin an cimma wannan buri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262