Manyan Mutanen da Sanata Natasha Ta Taba Zarga da Ci Mata Zarafi
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta samu kanta cikin dambarwa sakamakon abin da ya faru tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Taƙaddamar ta su ta fara ne bayan shugaban majalisar dattawan ya sauyawa sanatan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, wurin zama a majalisa.

Source: Twitter
Taƙaddamar Akpabio, Natasha ta kai kotu
Sanata Natasha-Uduaghan ta ɗauki matakin kai shugaban majalisar dattawan ƙara a gaban kotu kan zargin ɓata mata suna, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin ƙarar da ta shigar, ta buƙaci kotu ta tilasta Sanata Godswill Akpabio ya biyata diyyar N100.3bn saboda ɓata mata suna.
Mutanen da Natasha ta zarga da cin zarafinta
Bayan shigar da Akpabio ƙara a kotu, daga baya ta zarge shi da yunƙurin ci mata zarafi ta hanyar neman ya yi lalata da ita.

Kara karanta wannan
Natasha: 'Yan siyasar Arewa sun huro wuta, suna so shugaban majalisa ya yi murabus
Sai dai, Akpabio ba shi ba ne na farkon babban mutumin da Sanata Natasha ta taɓa zarga da ci mata zarafi.
Ga jerinsu a nan ƙasa:
1. Godswill Akpabio

Source: Twitter
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya shiga jerin mutanen da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zarga da yunƙurin yin lalata da ita.
Sanatar a yayin wata hira da tashar Arise tv ta zargi Akpabio da yunƙurin yin lalata da ita a wani lokaci can baya.
Natasha ta bayyana cewa tana da ƙwararan hujjoji waɗanda za su tabbatar da zargin da take yi wa shugaban majalisar dattawan.
"Da farko, mun fara zuwa gidansa da ke garin Ikot Ekpene. Sannan mu ka je wani gidansa da ke birnin Uyo, yana riƙe da hannuna, muka riƙa zagaya gidan, ɗaki bayan ɗaki, yana nuna mun yadda gidan ya ƙayatu."
"Ya kai ni wani kayataccen falon sauke baƙi, inda ya tambaye ni ko gidansa ya burge ni. Na ce masa ƙwarai kuwa, ranka ya daɗe, ɗakunan sun yi kyau sosai."
"Sai ya ce da ni, yanzu kin zama sanata, zan riƙa ware lokacin da za mu riƙa zuwa nan muna hutawa. Za ki ji dadin hakan. A wannan gabar ne, na janye daga gare shi, saboda ban fahimci abin da yake nufi ba."
- Sanata Natasha Akpoti
Wannan zargin na ta dai, ya jawo cece-kuce inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakinsu a kai.
2. Reno Omokri

Source: Facebook
A shekarar 2014, Sanata Natasha ta zargi tsohon hadimin Shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri da ci mata zarafi, cewar rahoton jaridar TheCable.
A wancan lokacin, Natasha ta rubuta a shafinta na Facebook cewa Reno Omokri ya ci zarafinta a wajen liyafar da aka shiryawa shugaban ƙasar Kenya, Uhuru Kenyatta.
Reno Omokri ya fito ya kare kansa, ya yi alƙawarin ba da kyautar $50,000 ga duk wanda ya kawo hotonsa ko bidiyonsa wanda zai nuna cewa yana wajen wannan taron.
Tsohon hadimin na Jonathan ya bayyana cewa a lokacin ba ya ƙasar, domin an tura shi Amurka domin halartar wani taro.
Daga baya, Natasha ta bi duka shafukanta na sada zumunta ta goge zargin da ta yi wa Reno Omokri na cin zarafinta.
3. Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan
A shekarar 2020, Natasha Akpoti ta zargi mijinta na yanzu da take mata haƙƙi da cin zarafinta, kamar yadda DeeOneAyekoto ya sanya a shafinsa na X.
Natasha ta zargi, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan wanda ke riƙe da sarautar Elema na masarautar Warri, da laifin cin zarafinta ta hanyar laƙada mata duka.
Ta bayyana cewa dukan da ya yi mata ya sanya ta yi ɓarin cikin da take da shi a wancan lokacin. Ta kuma zarge shi da sanya mata guba a abinci.
Sanatar ta kuma zarge shi da cinye mata kuɗi waɗanda ta ranta masa da suka kai N400m.
Atiku ya magantu kan rikicin Akpabio da Natasha
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha ta yi a kan Godswill Akpabio.
Atiku Abubakar ya buƙaci gudanar da sahihin bincike kan zarge-zargen da sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta yi, a kan shugaban majalisar dattawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

