Bola Tinubu Ya Ware Sama da Naira Biliyan 700 a Watan Azumi, Za a Yi Muhimman Ayyuka

Bola Tinubu Ya Ware Sama da Naira Biliyan 700 a Watan Azumi, Za a Yi Muhimman Ayyuka

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware kudi N733bn domin gudanar da aikin wasu manyan tituna a Najeriya
  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan fitowa daga taron Majalisar zartarwa (FEC) a Abuja ranar Litinin
  • Umahi ya ce titin Abuja zuwa Kano ne wanda zai laƙume kaso mafi tsoka daga cikin ƙuɗin da aka ware a wannan karon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da ware Naira biliyan 733 domin aiwatar da manyan ayyuka huɗu a fadin kasar nan.

Hakan wani yunkuri ne na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta hanyoyin mota da sauran muhimman ababen more rayuwa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya amince da ware N733bn domin aiwatar da wasu ayyuka a Najeriya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ministan Ayyuka, David Umahi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka gudanar a Abuja, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, an jero sunayensu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu za ta kashe N733bn

Ya bayyana cewa an raba wadannan kudade ga muhimman ayyuka hudu, ciki har da faɗaɗa manyan hanyoyi da kuma gadar Abakpa a jihar Enugu.

Umahi ya jero ayyukan da za a yi da suka haɗa da titin Odupani-Itu-Ikot Ekpene a jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom, zai laƙume N55 biliyan.

Ministan ya ce:

"Gwamnatin tarayya ta fara wannan aikin a shekarar 2021 amma daga bisani aka sake dubawa don rage yawan kudin aikin.
"Sai kuma titun Ibadan-Ilorin, sashe na 2 (Oyo-Ogbomoso, Jihar Oyo) wanda zai laƙume N147 biliyan. Za a faɗaɗa titin mai tsawon kilomita 147 don sauƙaƙa zirga-zirga."

Tinubu zai karisa titin Abuja zuwa Kano

Umahi ya ƙara da cewa majalisar zartarwa ta amince da ware Naira biliyan 507 domin karisa titin Abuja-Kaduna-Zaria har zuwa Kano mai tsawon kilomita 164.

A cewarsa, wannan titi ne zai wawushe kaso mafi tsoka daga cikin kuɗin da gwamnatin tarayya ta ware domin aiwatar da muhimman ayyuka a wannan karon.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban Majalisa ya goyi bayan kudirin ƙirkiro jiha 1 a Arewa, an faɗi sunanta

David Umahi ya ce an ware Naira biliyan 24 domin gina gadar Abakpa a jihar Enugu) wanda zai rage cunkoson ababen hawa a kusa da sansanin rundunar sojojin Najeriya na 82.

Umahi a wurin aiki.
Ministan ayyuka ya jero titunan da za a gina da N733bn Hoto: Dave Umahi
Asali: Facebook

Umahi ya kore nuna wariya a ayyukan

Ministan ayyukan ya yi karin haske kan yadda aka rarraba ayyukan, yana mai cewa ba a nuna bambancin yanki ba a ayyukan.

"Akwai lokacin da muka gabatar da wasu ayyuka, sai wani Sanata ya ce an fi ware wa yankin Kudu fiye da Arewa. Wannan ba gaskiya ba ne, domin Majalisar zartarwa tana amincewa ne da duk aikin da aka gabatar mata."

Ya kara da cewa yawancin ayyukan ba sababbi ba ne, gadar su aka yi daga gwamnatocin da suka gabata, kuma Shugaba Tinubu yana da burin ƙarisa su.

Umahi ya bukaci ‘yan Najeriya da su fahimci cewa gwamnati tana aiki tukuru wajen inganta hanyoyin sufuri, wanda hakan zai saukaka zirga-zirga da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin man fetur, an fara maganar karya farashin siminti a Najeriya

Tinubu ya naɗa shugaban NYSC

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Tinubu ya amince da nadin Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC).

Nadin na zuwa ne a daidai lokacin da masu bautar kasa ke ci gaba da kiran gwamnatin tarayya da ta biya su sabon mafi karancin albashi na ₦77,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262