Talaka Ya Samu Bulus: Gwamnan Kano Ya Karya Farashin Na'ukan Abinci 17

Talaka Ya Samu Bulus: Gwamnan Kano Ya Karya Farashin Na'ukan Abinci 17

  • Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf tare da hadin gwiwar manyan ‘yan kasuwa sun rage farashin kayan masarufi
  • Rahotanni sun nuna cewa ana samun ragin har zuwa N13,000 kan wasu kayayyaki da ake sayarwa a shaguna a wajen baje kolin
  • Gwamnatin Kano ta bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin saukaka wa al’umma, musamman lokacin azumin watan Ramadan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shiri na rage farashin kayan masarufi a wajen baje kolin karya farashi domin tallafa wa al’umma.

Matakin ya samu goyon bayan manyan ‘yan kasuwan Kano, wanda hakan ya taimaka wajen rage farashin kayan abinci kamar shinkafa, sukari, fulawa da mai.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, NNPCL ya yi maganar saukar farashin fetur da kara gidajen mai

Abba Kabir
Gwamnan Kano ya karya farashin abinci. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Hadimi a gwamnatin Kano ya wallafa yadda aka karya farashin na'ukan kayan abinci daban daban a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke tsaka da azumin watan Ramadan, domin saukaka musu rayuwa.

Rage farashin muhimman kayan abinci

A sabon tsarin, ana samun saukin farashin wasu kayayyaki kamar haka:

  • Shinkafar BUA: Daga N81,000 zuwa N76,000
  • Shinkafar Amarava: Daga N72,000 zuwa N66,000
  • Sukarin Dangote: Daga N82,000 zuwa N79,000
  • Fulawar IRS: Daga N61,000 zuwa N57,000

Haka nan, kayan girki irin su taliya da macaroni suma an rage musu farashi. Misali:

  • Taliya Crown: Daga N16,000 zuwa N15,100
  • Macaroni Crow: Daga N15,700 zuwa N14,700
  • Macaroni BUA: Daga N16,500 zuwa N15,000

Sauke farashin hatsi da mai

Haka nan, man girki wanda ke da muhimmanci a girkin yau da kullum, suma an rage musu farashi kamar haka:

Kara karanta wannan

Ana shirin fara azumin Ramadan, mutane sama da 15 sun mutu a jihar Katsina

  • Mai kamfanin Excellent lita 25 : Daga N79,000 zuwa N70,000
  • Mai kamfanin Kings: Daga N79,000 zuwa N72,000
  • Mai kamfanin OKI: Daga N70,000 zuwa N66,000

Kazalika, kayan amfanin gona kamar wake, gero, da masara suma an rage su:

  • Wake kwano 40: Daga N105,000 zuwa N92,000
  • Masara kwano 40: Daga N55,000 zuwa N52,000
  • Buhun albasa: Daga N60,000 zuwa N45,000
Gwamnatin Kano
Jami'an gwamnatin Kano na rabon kayan abinci. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Dalilin rage farashin da tasirinsa ga jama’a

Ana ganin saukin farashin zai taimaka wajen rage radadin tsadar abinci da mutane ke fuskanta a halin yanzu.

Masana sun bayyana cewa rage farashin kayan abinci zai taimaka wajen tabbatar da wadatar kayayyaki a kasuwa, kuma hakan zai rage hauhawar farashi a shagunan sayar da abinci.

Gwamnatin Kano ta bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan dama domin sayen kayan abinci a farashi mai rahusa a Trade Fair Complex .

Kara karanta wannan

Ramadan: An Yi Bikin Karya Farashin Kayan Abinci a Jihar Kano

Gwamnonin jihohi da dama a Arewa na kokarin sauke farashi a watan Ramadan domin kawo saukin rayuwa ga al'umma.

Sanata Yari ya yi rabon abinci a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari ya raba tirelolin abinci 496 a dukkan kananan hukumomin jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa Sanatan ya bayyana cewa za a dauki matakan tabbatar da cewa abincin ya isa ga mabukata na hakika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng