Barayi Sun Yi Taurin Ido ana Sallar Tarawi, Sun Je Masallaci Sun Yi Sata

Barayi Sun Yi Taurin Ido ana Sallar Tarawi, Sun Je Masallaci Sun Yi Sata

  • Wasu barayi sun sace babura guda uku yayin sallar Tarawihi a wani masallaci da ke Tipper Garage a Kuje a Abuja
  • Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda masu baburan suka ankara da sace musu su jim kadan bayan kammala sallah
  • An kai rahoton lamarin ga ‘yan sintiri da kungiyar masu babura, amma ‘yan sanda sun ce ba su samu labarin satar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun sace babura guda uku yayin da ake tsaka da sallar tarawi a wani masallaci da ke Tipper Garage a yankin Kuje na Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa satar baburan ta faru ne a ranar Asabar, lokacin da al’ummar Musulmi ke yin ibada a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya yi gargadi kan siyasantar da tsaro bayan kalaman El-Rufa'i

Abuja
An sace babura ana sallar tarawi a Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya bar jama’a cikin fargaba, inda aka sanar da ‘yan sintiri da kungiyar ‘yan acaba domin kokarin gano baburan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace babura ana sallar tarawi a Abuja

Wani mazaunin yankin, Ibrahim Jamilu, wanda ya halarci sallah a masallacin, ya ce bayan an idar da sallah ne wasu mutane uku suka yi kururuwar cewa an sace musu babura.

Jamilu ya bayyana cewa baburan sun bace ne ba tare da kowa ya lura da satar ba, yayin da ake tsaka da ibada.

A cewarsa, satar babura ta zama ruwan dare a wasu yankunan Kuje, musamman lokacin taron jama’a kamar sallah da bukukuwa.

Ya ce jama’a na fargabar yadda masu aikata wannan laifi ke samun damar sace babura ba tare da an ankara ba.

An kai rahoto ga ‘yan sintiri da 'yan acaba

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Dalibar jami'a ta mutu a hannun yan bindiga duk da biyan miliyoyi a Zamfara

Bayan faruwar lamarin, masu baburan sun garzaya wajen ‘yan sintiri da ke kula da yankin domin sanar da su abin da ya faru.

Haka kuma, kungiyar masu babura ta Kuje ta ce za ta taimaka wajen binciken inda baburan suka shiga da kuma ko za a iya gano su.

Sai dai duk da haka, rahotanni sun nuna cewa lamarin bai kai ga rundunar ‘yan sanda da ke yankin ba.

Wani jami’in ‘yan sanda da aka tuntuba ya ce ba su samu rahoton satar ba, a kan haka aka bukaci wadanda aka sace wa baburan su kai rahoto domin daukar matakin da ya dace.

Fargaba kan yawaitar satar babura

Wasu daga cikin mazauna yankin sun nuna damuwa kan yadda satar babura ke karuwa a Kuje, musamman a wuraren taruwar jama’a.

Wani mai abinci a yankin ya ce:

“Yana da matukar muhimmanci masu babura su kasance masu taka tsantsan, musamman lokacin sallah, domin ‘yan daba na bibiyar inda za su yi satar.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

Jama’a sun bukaci hukumomin tsaro su kara daukar matakan kare al’umma daga irin wadannan ayyuka na bata-gari.

Masallacin kasa
Sashen masallacin kasa na Abuja. Hoto: Muhammad Ali Adam
Asali: UGC

Haka kuma, sun bukaci a samar da karin tsaro a kusa da masallatai domin kare dukiyoyin jama’a yayin sallar tarawi.

'Yan bindiga sun sace mutane a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Abuja sun sace wasu mutane a kusa da barikin sojoji.

Dakarun rundunar 'yan sanda sun samu mota a kusa da wajen da abin ya faru kuma ana zaton motocin na mutanen da aka sace ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng