Dangote Ya Ragewa 'Yan Kasuwa N16bn domin Sauke Farashin Fetur a Najeriya
- Matatar Dangote ta bayyana cewa za ta dauki asarar Naira biliyan 16 domin rage wa 'yan Najeriya wahalar tsadar fetur
- Dangote zai mayar da N65 kan kowacce lita ga dillalan da suka saye man fetur a tsohon farashi kafin sabon ragin da matatarsa ta yi
- A kan haka, Dangote ya gargadi dillalai da su guji cin gajiyar sabon tsarin ta hanyar sayar da fetur a farashi mai tsada ga 'yan kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matatar Dangote ta dauki matakin tallafawa ‘yan Najeriya ta hanyar rage farashin man fetur da kuma bayar da ragin N65 ga dillalai da suka saye fetur kafin ya rage farashi.
Sabon tsarin rage farashin ya zo ne bayan kamfanin Dangote ya saukar da farashin lita daga N890 zuwa N825 a matatarsa da ke Legas.

Asali: Getty Images
Rahoton Channels Television ya nuna cewa wannan mataki yana daga cikin kokarin Dangote na tallafawa tattalin arzikin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote zai rage wa 'yan kasuwa asara
A wata sanarwa da matatar Dangote ta fitar a karshen mako, Dangote ya tabbatar da cewa zai mayar da N65 kan kowacce lita ga dillalan da suka sayi fetur a tsohon farashi.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da cewa rage farashin ya shafi dukkan ‘yan Najeriya cikin gaggawa domin su amfana da saukin farashin kamfanin.
Matatar Dangote ta ce wannan tallafi zai shafi sama da ton 200,000 na fetur da aka saya a tsohon farashi.
"A tunaninmu, babu wanda ya kamata ya yi asara sakamakon wannan sabon farashin, kuma dole ne ‘yan Najeriya su amfana kai tsaye da rage farashin,"
- Matatar Dangote
Dangote ya gargadi 'yan kasuwar fetur
Dangote ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wasu dillalai ke sayar da fetur da tsada duk da rage farashin da aka yi musu.
Kamfanin ya ce sayar da fetur a farashi sama da N900 bayan rage farashin zuwa N825 tamkar zalunci ne ga ‘yan Najeriya.
The Cable ta rahoto matatar Dangote ta ce:
"Matatar Dangote ba za ta yarda wasu dillalai su ci gajiyar rage farashin fetur su sayar da shi da tsada ba. Wannan abu ne da zai kara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala,"
A kan haka Dangote ya bukaci masu sayen fetur da su rika bin diddigin farashi don kauce wa cin zarafin su.
Kamfanin ya ce wadanda suka saye fetur a tsohon farashin a tashoshin AP, Heyden, ko MRS za su iya kai koken su tare da takardar shaidar sayan fetur domin a biya su kudin da aka rage.

Asali: UGC
Dangote ya jaddada cewa a karkashin sabon farashin, babu dalilin da zai sa wani dan Najeriya ya biya sama da N900 kan kowacce litar fetur.
Kamfanin ya ce yana nan daram a kan burin sa na samar da man fetur mai inganci kuma mai saukin farashi domin tallafawa tattalin arzikin Najeriya.
MRS ya rage farashin fetur a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man fetur na MRS ya bayyana cewa ya rage kudin man fetur a fadin kasar nan.
Kamfanin MRS ya ce ya rage kudin ne domin saukin da matatar Dangote ta musu a sanadiyyar fara azumin watan Ramadan na 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng