Ramadan: Hukumar Hisbah Ta Ci Gaba da Aikin Allah cikin Watan Azumi a Kano
- Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kano sun yi caraf da wasu matasa da ake zargi da laifin ƙin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan
- Hukumar ta cafke matasan ne yayin da jami'anta suka gudanar da sintiri a wurare daban-daban na cikin birnin Kano
- Jami'an hukumar sun kuma cafke masu askin banza tare da direbobin keke Napep masu haɗa maza da mata a cikin kekunansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar Hisba a jihar Kano ta cafke wasu matasa da ake zargi da keta dokokin Musulunci.
Hukumar Hisbah ta cafke matasan ne saboda zargin rashin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma.

Asali: Twitter
Mataimakin shugaban hukumar Hisba, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da wannan kamen ga manema labarai a cikin jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe aka kama mutanen?
Ya bayyana cewa an kama masu laifin ne yayin gudanar da ayyukan sintiri na yau da kullum da jami’an Hisba suka yi a wurare daban-daban na birnin Kano.
Hakanan, hukumar ta kama kusan mutane 60 da suka yi askin banza waɗanda ba su dace ba, wanda ya saɓa da dokokin addinin Musulunci da kuma al’adun malam Bahaushe.
Wannan kuma ya zama wani ɓangare na kokarin hukumar na tabbatar da kiyaye ɗabi'un addini da na al'ada a cikin jihar.
Hisbah ta cafke masu keke Napep
Bugu da ƙari, jami'an Hisba sun kama wasu direbobin keken Napep da ake zargi da haɗa mata da maza cikin kekunansu, wanda hukumar ta bayyana cewa ba za ta lamunta ba.
Wannan yana cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da cewa dokokin Shari’a suna aiki yadda ya kamata cikin al’umma, musamman a lokacin azumin Ramadan.
Hukumar ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da sintiri a duk fadin jihar domin tabbatar da bin doka da oda, da kuma tabbatar da cewa dukkanin al’umma suna kiyaye dokokin Shari’a a lokacin wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Kara karanta wannan
Kano da jihohin Arewa sun fara azumin Ramadan da ƙafar dama, Saudi ta turo tallafi
Wannan ya nuna cewa Hisba tana aiki tuƙuru kan sanya ido game da yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu a cikin wannan lokaci na watan Ramadan.
Hisbah za ta ci gaba da ayyukanta
Kamar yadda aka saba, hukumar na ƙara daukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa dukkan al’umma suna kiyaye dokokin addinin Musulunci da al’adunsu yayin wannan lokaci mai muhimmanci.
Duk da haka, hukumar ta kara jaddada cewa tana da niyyar ganin jama'a na bin doka da oda har zuwa ƙarshen watan Ramadan.
Gwamnatin Kano za ta yi ciyarwa a Ramadan
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ware kuɗaɗe domin gudanar da shirin ciyarwa a cikin watan azumin Ramadan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware N8bn domin gudanar da shirin na ciyar da jama'a a lokacin azumi.
Asali: Legit.ng