Gwamnatin Kano Ta Ware Kudin Ciyarwa a Ramadan, Ta Fadi Abin da Za Ta Kashe

Gwamnatin Kano Ta Ware Kudin Ciyarwa a Ramadan, Ta Fadi Abin da Za Ta Kashe

  • Gwamnatin jihar Kano za ta gudanar da shirin ciyar da al'umma a lokacin azumin watan Ramadan na wannan shekarar
  • Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware Naira biliyan takwas (N8bn) domin gudanar da shirin
  • Gwamnan na Kano ya yi nuni da cewa watan azumin Ramadan na bana ya zo a daidai wani mawuyacin lokaci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shirya gudanar da shirin ciyarwa a watan Ramadan.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware Naira biliyan takwas (N8bn) domin shirin ciyar da al’umma a wannan watan na Ramadan.

Gwamnatin Kano za ta yi ciyarwa a Ramadan
Gwamnatin Kano za ta gudanar da shirin ciyarwa a Ramadan Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 1 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Kano da jihohin Arewa sun fara azumin Ramadan da ƙafar dama, Saudi ta turo tallafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saudiyya ta ba tallafin dabino

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da rabon katan-katan 1,250 na dabino da masarautar Saudiyya ta ba da gudunmawa, wanda aka gudanar a ɗakin Coronation Hall, fadar gwamnatin jihar Kano, a ranar Juma’a.

Gwamnan, wanda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya godewa jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Adamawi, bisa wannan kyautatawa.

Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na huɗu da jihar ke samun irin wannan gudunmawa ta dabino daga masarautar Saudiyya.

Ya ƙara da cewa wannan tallafi ya zo a daidai lokacin da gwamnatinsa ke ƙoƙarin samar da kayan abinci ga mabuƙata, duba da halin matsin tattalin arziƙi da jama’a ke fuskanta.

Ya bayyana cewa Kano ita ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya, lamarin da ya ja hankalin mutane da dama su zo su zauna a cikinta, wanda hakan kuma ya ƙara nauyi a kan gwamnatin, musamman a ɓangaren lafiya da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Bayan fara binciken zabtare albashi: Abba ya dakatar da shugaban ma'aikatan Kano

"Mai girma, wannan shekarar Ramadan ya zo a wani mawuyacin lokaci, yayin da jihar Kano ita ce kaɗai jihar zaman lafiya a Arewacin Najeriya, don haka nauyin da ke kan gwamnati, jama’a da kuma ababen more rayuwa yana da girma."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba ya miƙa buƙatarsa ga Saudiyya

Gwamnan ya roƙi masarautar Saudiyya da ta zo ta gina asibitin masu taɓin hankali da kuma gyaran sansanin yara marasa galihu a jihar domin inganta rayuwar waɗannan mutanen.

Gwamna Abba Yusuf ya nuna jin dadinsa kan kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin masarautar Saudiyya da al’ummar Kano, yana mai alƙawarin ƙara ƙarfafa wannan dangantaka domin amfanin gwamnatocin biyu.

A nasa jawabin, Jakadan Saudiyya, Ahmad Adamawi, ya tabbatar da kudirin masarautar Saudiyya na ci gaba da bayar da tallafin jin ƙai ga gwamnatin jihar Kano.

Ya yabawa Gwamna Abba Yusuf bisa manyan ayyukan da yake aiwatarwa a jihar, musamman a ɓangaren lafiya, ilimi da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya samu goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2027

Farashin abinci ya sauka a Ramadan

A wani labarin kuma, kun ji cewa farashin kayyyakin abinci na ci gaba da sauka a jihihon Arewa yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewa farashin kayan abinci yafi raguwa ne a jihohin da ake noma mafi yawan kayayyakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel