'Ba Fadanki ba ne': Natasha Ta Ja Kunnen Matar Akpabio, Ta Fadi Shirinta kan Zarginsa
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta mayar da martani ga mai dakin Godswill Akpabio kan zargin da take yi masa
- Natasha ta bukaci Ekaette Akpabio ta nesanta kanta daga takaddamar da ke tattare da tuhumar cin zarafi da ake yi wa mijinta
- Rigimar ta fara ne tun lokacin da Natasha ta ki zama a wurin da aka tanada mata a majalisa, sannan ta fara wasu babatu
- A wasikar da ta aika wa matar Akpabio, Natasha ta bukaci ta bar mijinta ya kare kansa, tana cewa tana da hujjoji masu karfi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja -Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci matar Shugaban Majalisar Dattawa, Ekaette Akpabio ta kame bakinta kan zargin mijinta da take yi.
Sanata Natasha ta bukaci Ekaette ta nesanta kanta daga takaddamar da ke tattare da tuhumar cin zarafi da tsoratarwa da ake yi wa mijinta, Godswill Akpabio.

Asali: Twitter
Zargin da Natasha ke yi wa Akpabio
A wasikar da ta aika wa matar Akpabio ta hannun lauyanta, Victor Giwa, Natasha ta bukaci ta guji shiga cikin wannan takaddama, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan zargin da Natasha ta yi cewa Akpabio ya neme ta da lalata, kuma ta nuna ta ce ta ki amincewa da buƙatarsa.
Natasha ta ce rashin amincewarta ya jawo mata hantara da bijirewa kudurorin da ta kawo majalisa wanda Akpabio ke jagoranta.
Matar Akpabio ta kalubalanci Sanata Natasha
Bayan zarge-zargen nata, matar shugaban majalisar dattawa, Ekaette Akpabio ta fito ta kare mijinta, ta ce babu gaskiya kan zargin saboda mutum ne mai mutunci.
Ekaette ta fadi irin alakar da ke tsakanin iyalanta da kuma Uduaghan tun ma kafin ya auri Sanata Natasha, ta ce mijinta ba zai taba yin haka ba.
Wasikar Sanatar mai taken "Guji Shiga Maganar Cin Zarafi da Ake Zargin Shugaban Majalisar Dattawa," ta jaddada cewa Akpabio ya kamata ya kare kansa da kansa.
Natasha ta ce:
"Ki na son janyo kanki cikin wannan matsala, kuma Natasha tana so ki nesanta kanki daga wannan batu."

Asali: Instagram
Natasha ta ja kunnen matar Godswill Akpabio
Sanata Natasha ta ce tana da hujjoji da za ta tabbatar da zargin da take yi, tana mai shawartar Ekaette Akpabio da ta bar mijinta ya kare kansa.
Ta kara da cewa:
"Natasha tana da hujjoji masu karfi, muna shawartarki ki bar Shugaban Majalisar ya kare kansa domin ki kula da lafiyarki da iyalanki."
Sanatar ta nanata cewa ta himmatu wurin kare hakkin mata a Najeriya, tana mai cewa ta kuduri aniyar kare kimar iyali da al’umma, Vanguard ta ruwaito.
Yadda Natasha ta zargi Omokri a 2014
A baya, kun ji cewa an tono yadda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi Reno Omokri da nemanta da lalata yayin wani taro a Abuja.
Sanata Natasha ta yi wannan zargin ne lokacin Omokri yana a matsayin hadimi na musamman ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan
'Ba haka ba ne': Matar Akpabio ta yi barazana ga Natasha, ta fallasa tsohuwar alakarsu
Sai dai Omokri ya musanta labarin, ya kawo hujjojinsa cewa a lokacin da take magana bai kasar Najeriya tare da ba da kyautar dubban daloli ga wanda ya kawo hujja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng