Azumin Ramadan: Atiku Abubakar Ya Tura Muhimmin Sako ga Gwamnatin Tarayya
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi magana kan halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a halin yanzu
- Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran mahukunta a dukkanin matakai da su sauƙaƙa kan raɗaɗin da ake ji
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP ya kuma yi kira ga jama'a da su taimakawa junansu musamman a watan Ramadan
- Wazirin Adamawa ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa sanya ƙasar nan cikin addu'o'insu a cikin wata mai alfarma na Ramadan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta yayin da aka fara azumin watan Ramadan.
Atiku Abubakar ya buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai da su ɗauki matakai na musamman domin rage wahalhalun da ƴan Najeriya ke sha.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban ƙasan na Najeriya ya sanya a shafinsa na X a Juma'a, 28 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya buƙaci a tausayawa ƴan Najeriya
Atiku ya jaddada muhimmancin bayar da taimako, inda ya yi kira ga ƴan Najeriya su taimakawa mutanen da suke da buƙata.
"Ƴan Najeriya na fuskantar mawuyacin yanayin tattalin arziki, kuma yana da muhimmanci gwamnatoci su samar da tallafi don taimakawa mutane da saukaka yanayin rayuwarsu."
"Ya kamata rayuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) ta zama abin koyi a garemu, domin ya koya mana amfanin yawan bayar da taimako, musamman a cikin watan Ramadan."
- Atiku Abubakar
Atiku ya ba ƴan Najeriya shawara
Atiku Abubakar ya yi kira ga al'ummar musulmai da sauran ƴan Najeriya su yi amfani da watan Ramadan a matsayin dama ta bayar da sadaka, tausayi, da addu'o'i domin ci gaban ƙasa, zaman lafiya, da bunƙasar al'umma.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan kuma babban jigo a jam'iyyar PDP ya tabbatar da cewa watan Ramadan lokaci ne na komawa ga Allah tare da neman haɗin kan ƙasa.
"Ina roƙon mu tuna da Najeriya a cikin addu'o'inmu tare da kira ga gwamnatoci su samar da taimakon da ya kamata wanda zai saukaka raɗaɗin rayuwar ƴan Najeriya a lokacin azumin Ramadan da bayan wucewarsa."
- Atiku Abubakar
Atiku ya naɗa sabon hadimi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya naɗa sabon mai taimaka masa kan harkokin matasa.
Atiku Abubakar ya ɗauko Tahir Tanimu Tahir ya ba shi muƙamin mai taimaka masa na musamman kan harkokin matasa da tsare.
Tahir Tanimu Tahir ya taɓa yin aiki a ƙarƙashin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a wa'adin farko na mulkinsa, ya riƙe muƙamin mataimaki na musamman kan harkokin rediyo.
Matashin dai ya fito ne daga ƙauyen Marama na ƙaramar hukumar Hawul a jihar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng