Ana cikin Azumi Mummunar Gobara Ta Lakume Babbar Kasuwa a Sokoto

Ana cikin Azumi Mummunar Gobara Ta Lakume Babbar Kasuwa a Sokoto

  • An shiga jimami a jihar Sokoto bayan wata mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Kara
  • Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 1 ga watan Maris yayin da al'ummar musulmi suka fara gudanar da azumin watan Ramadan
  • Shagunan ƴan kasuwa da dama sun ƙone ƙurmus yayin da wasu suka yi ƙoƙarin ganin sun fitar da kayayyakinsu domin kaucewa wutar
  • Jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Sokoto sun garzaya kasuwar domin ƙoƙarin hana wutar bazuwa zuwa wasu yankunan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - An samu tashin mummunar gobara a kasuwar Kara, da ke birnin Sokoto na jihar Sokoto.

Gobarar dai ta shafi kasuwar ne wacce ta kasance shahararriya da ake sayar da hatsi da sauran kayayyaki.

Gobara ta tashi Sokoto
Gobara ta lakume shaguna a kasuwar Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gobarar ta tashi ne a safiyar ranar Asabar, inda ta mamaye kasuwar.

Kara karanta wannan

Dakaru sun yi dirar mikiya a kan 'yan ta'adda ana tsaka da karbar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara ta yi ɓarna a kasuwar Sokoto

Gobarar ta cinye shaguna da wuraren ajiyar hatsi, ta hanyar ƙone su ƙurmus.

Har yanzu ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, amma jami’an hukumar kashe gobara na jihar Sokoto suna ci gaba da ƙoƙarin shawo kan wutar.

Masu shaguna da mazauna gidaje kusa da kasuwar sun yi ta ƙoƙarin fitar da kayayyakinsu don gujewa illar da wutar ka iya haifarwa.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin babban manajan kasuwar, amma hakan bai yiwu ba, saboda yana can ƙoƙarin hana mutane yin amfani da wannan dama domin yin sata.

Gobarar dai ta haddasa asarar dukiya mai yawa, ƴan kasuwa da dama suka koka kan yadda wutar ta ƙone musu kayayyakinsu gaba ɗaya.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa gobarar ta zo masu a bazata, kuma ba su samu damar ceto komai daga shagunan su ba.

Hukumomi sun kai agajin kashe gobara

Kara karanta wannan

Sabuwar zanga zanga ta barke a Kano, an samu bayanai

Hukumomin jihar, ciki har da hukumar kashe gobara, na ci gaba da ƙoƙarin daƙile wutar don hana ta ƙara bazuwa zuwa wasu sassa na yankin.

Mutane da dama sun taru a kasuwar suna kallon yadda wutar ke ci gaba da ƙone shaguna, inda suka shiga jimami saboda irin ɓarnar da ta auku.

Gobarar kasuwar Kara na ƙara jaddada bukatar ɗaukar matakan kare kasuwanni daga irin waɗannan bala’o’i da ke haddasa asarar dukiya da lalata tattalin arziƙin ƴan kasuwa.

Gobara ta laƙume kasuwa a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobara a babbar kasuwar da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Gobara ta laƙume shagunan da ke sashen kayan abinci na fitacciyar kasuwar bayan an dawo da wutar lantarki a cikin tsakar dare.

Ƴan kasuwa da dama sun yi asara inda aƙalla shaguna sama da 103 suka ƙone ƙurmus sakamakon tashin da gobarar ta yi.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga, sun yi raga raga da miyagu

Mutane da dama waɗanda lamarin ya ritsa da su sun bunƙaci gwamatin jihar da ta kai musu ɗauki domin su farfaɗo daga asarar da suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng