Ramadan: 'Yan Sanda Sun Fitar da Gargadi ga Mutanen Kano kan Tsaro
- Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta taya al'ummar Musulmi murnar fara watan Ramadan tare da tabbatar da an dauki matakan tsaro
- An shawarci jama'a da su guji daukar kayan da ba su da muhimmanci yayin halartar sallar Tarawih, tare da kula da muhalli da bayar da rahoto
- An gargadi masu ababen hawa da su bi ka'idojin hanya, tare da hana yara kanana da wadanda ba su da lasisin tukin mota, babur ko Keke Napep
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta fitar da sanarwa tana taya al'ummar Musulmi murnar fara watan Ramadan, tare da tabbatar da cewa an dauki matakan tsaro na musamman.
Rundunar ta bayyana cewa ta dauki matakan ne don ganin an gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Asali: Facebook
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a Facebook cewa an yi tsare-tsare na musamman don tabbatar da tsaron al'umma a wannan lokaci mai muhimmanci ga Musulmi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakan tsaro da shawarwarin 'yan sandan Kano
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar an bayyana cewa an samu karuwar baƙi daga sassa daban-daban a lokacin Ramadan, don haka rundunar ta sake tsara dabarun tsaro.
An shawarci jama'a da su:
- Guji daukar dayan da ba su da muhimmanci: Masu halartar sallar Tarawih su guji daukar kayan da ba su da muhimmanci, sai dai tabarmar sallah kawai, don rage zargin da ka iya tasowa.
- Kula da Muhalli: Masu halartar masallatai da wuraren tafsiri su kasance masu kula da muhalli, tare da bayar da rahoto kan duk wani abu ko motsi da ake zargi ga hukumomin tsaro.
- Bin ka'idojin hanya: Masu abubuwan hawa su bi ka'idojin hanya, su guji tukin ganganci, gudun wuce kima, da yin tseren mota don rage hadurra.
- Hana yara kanana tuki: An hana yara kanana da wadanda ba su da lasisi tukin mota, babur ko Keke Kapep.
- Bukatar kulawar iyaye: Iyaye da masu kula da yara su tabbatar suna tare da manya yayin azumi don hana bacewa ko hadurra.
- Hana abubuwan fashewa: An haramta amfani da abubuwan fashewa kamar bangers da knockouts a lokacin Ramadan.
- Hana tarukan da ba a nemi izini ba: An hana tarukan da ba a nemi izini ba, kuma dole ne a nemi izini daga hukuma kafin gudanar da kowane taro.

Kara karanta wannan
Jama'a suna zaman ɗar-ɗar, jami'an tsaro da sulken yaki sun kewaye gidan sarki a Kano
Gargadi kan ayyukan daba a jihar Kano
Rundunar 'yan sanda ta gargadi cewa ba za ta yarda da duk wani nau'i na ayyukan daba a lokacin wannan wata mai alfarma ba.
Duk wanda aka samu yana aikata irin wadannan laifuffuka za a dauki mataki mai tsauri a kansa bisa tanadin doka.

Asali: Facebook
Hadin kai da bayar da rahoto
An bukaci jama'a su ci gaba da ba da hadin kai ga hukumomin tsaro, ciki har da FRSC, Hukumar Tsaro ta NSCDC, KAROTA, Hisbah, 'yan banga, da sauran kungiyoyin sa-kai.
Rundunar ta ce idan aka ga wani abu da ake zargi, a sanar da mafi kusa ofishin 'yan sanda ko a tuntubi rundunar 'yan sanda ta Jihar Kano ta hanyar:
Lambobin Gaggawa:
- 08032419754
- 08123821575
- 09029292926
Baya ga haka, rundunar ta ce za a iya tuntubarta ta kafofin sada zumunta kamar Facebook, X, Instagram da sauransu.
Ramadan: An rage kudin abinci a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an shirya baje kolin karya kayan abinci a wata kasuwa a jihar Kano saboda shigowar Ramadan.
Rahotanni sun nuna cewa masu sayayya sun samu rangwame a kan yadda ake sayar da kayayyaki a sauran kasuwanni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng