Bala Lau Ya Buɗe Katafaren Masallacin da Ɗan Majalisa Ya Gina a Kano, An Raɗa Masa Suna

Bala Lau Ya Buɗe Katafaren Masallacin da Ɗan Majalisa Ya Gina a Kano, An Raɗa Masa Suna

  • Ɗan Majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Bichi, Abubakar Kabir Abubakar ya gina katafaren masallaci na biliyoyin Naira da islamiyya
  • Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jagoranci kaddamar da masallacin a Bichi ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025
  • Ɗan majalisar ya bayyana cewa ya gina masallaci da islamiyyar ne domin ƙara inganta harkokin ibada da koyon ilimin addinin Musulunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya kaddamar da sabon Masallacin Juma’a a Bichi.

Shugaban JIBWIS da aka fi sani da Izala ya buɗe sabon masallacin tare da makarantar Islamiyya da Hon. Abubakar Kabir Abubakar, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi ya gina.

Sheikh Bala Lau.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ƙaddamar da sabon masallaci a jihar Kano Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an buɗe sabon masallacin ne ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025 a yankin Bichi da ke Arewacin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sheikh Guruntum ya gina katafaren masallaci, jama'a sun cika wajen bude shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An raɗa wa sabon masallacin suna

Katafaren Masallacin da ke kan hanyar Gwarzo a Bichi (B) ya samu sunan marigayi Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi, babban malamin addinin Musulunci kuma alkali.

Wannan aiki ya kunshi masallacin Juma’a, makarantar Islamiyya, da dakunan bayan gida domin amfanin jama’a.

Da yake jawabi a taron, Hon. Abubakar Kabir Abubakar ya bayyana cewa gina masallacin da makarantar Islamiyya na daga cikin burinsa na bunƙasa ilimin addinin Musulunci a yankin Bichi.

Ya kara da cewa, baya ga wannan aiki, ya gina makarantu, tituna, asibitoci, da gadar ruwa domin inganta rayuwar al’umma a mazabarsa.

Manyan bakin da suka halarci bude masallacin

Taron buɗe sabo kuma katafaren masallacin ya samu halartar manyan malamai da ‘yan siyasa daga ciki da wajen Kano.

Daga cikin su akwai shugabn Izala na Kano, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, wanda shi ne shugaban hukumar kula da alhazai ta ƙasa (NAHCON).

Sauran sun haɗa da sakataren kungiyar Izala na ƙasa, Sheikh Muhammad Kabiru Gombe, shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, da ƴan majalisa da dama.

Kara karanta wannan

"Karya kake yi," Ƴan Majalisa 36 sun ƙara yi wa kakaki bore, sun tabbatar da tsige shi

Haka nan kuma manyan ƴan siyasa da ƴan kasuwa daga sassa daban-daban na jihar Kano sun halarci wannan taron kaddamar da sabon masallaci da makarantar islamiyya.

Masallacin Sheikh Abubakar Gumi.
Sheikh Bala Lau ya kaddamar katafaren masallacin Juma'a da ɗan Majalisa ya gina a Kano Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Mazauna Bichi sun nuna farin ciki

Wannan katafariyar cibiyar koyar da addinin Musulunci da ilimi wata gagarumar gudunmawa ce ga al’ummar Bichi musamman a wannan lokaci da aka shiga watan azumi.

Mazauna mazaɓar Bichi sun nuna tsantsar farin cikinsu bisa yadda ɗan Majalisar ya gina waɗannan wurare da za su yi ibada kuma su koyi ilimin da zai amfane su duniya da lahira.

Ɗan majalisa ya raba tallafin Ramadan

A wani rahoton, kun ji cewa ana shirin fara azumin watan Ramadan, ɗan majalisar tarayya a Sakkwato, Hon. Sani Alhaji Yakubu ya ba da tallafin makudan kudi ga yan mazabarsa.

Ɗan majalisar ya rabawa al'ummarsa tallafin kudi Naira miliyan 40 da buhunan shinkafa 1000 domin rage masu radaɗin halin matsin da ake ciki a watan Ramadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262