Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Sake Fitar da Sanarwa gabanin Fara Azumin Ramadan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Sake Fitar da Sanarwa gabanin Fara Azumin Ramadan

  • Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci masu hannu da shuni su tallafawa mabukata albarkacin watan Ramadan
  • A wata sanarwa da NSCIA ta fitar ranar Alhamis, Sultan ya roƙi ƴan kasuwa su daina ɓoye kayan abinci kuma su rage farashi domin sauƙaƙawa masu azumi
  • Wannan dai na zuwa ne bayan fadar sarkin Musulmi ta ba da umarnin fara duban jinjirin watan Ramadan daga yau Juma'a, 28 ga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Yayin da musulmi a faɗin duniya ke shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan, an roƙi ƴan kasuwa a Najeriya su rage farashin kayan abinci.

Majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) karkashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ta buƙaci ƴan kasuwa su tausaya wa jama'a.

Kara karanta wannan

Bayan duba wata, Sarkin Musulmi ya fadi ranar fara azumin Ramadan a Najeriya

Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi ya bukaci yan kasuwa su rage farashin abinci kafin ramadan Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Sarkin musulmi ne ya yi wannan kira ga ƴan kasuwa a wata sanarwa da sakataren NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yau za a fara duban watan Ramadan

Wannan kira na zuwa ne bayan fadar sarkin Musulmi ta bukaci a fara duban jinjirin watan Ramadan daga yau Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2028 wanda ya zo daidai da 29 ga watan Sha'aban, 1446H.

Idan Allah ya sa aka ga watan a yau Juma'a, sarkin Musulmi zai sanar da al'umma su tashi da azumi ranar Asabar, 1 ga watan Maris. 2025.

Idan kuma watan ya ɓuya, to Sha'aban zai cika 30 sannan Musulmi za su fara azumi ranar Lahadi, 2 ga watan Maris.

A halin yanzu dai al'ummar musulmi a Najeriya na dakon sanarwa daga fadar mai alfarma sarkin Musulmi yau Juma'a da daddare.

Da yake jan hankalin kafin fara azumi, Sultan ya buƙaci ƴan kasuwa su tausayawa mutane albarkar wannan wata, su rage farashin kayan abinci.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta sanar da ranar da musulmi za su fara azumin watan Ramadan

Sultan ya buƙaci a taimaki mabuƙata

Sarkik Musulmi ya yi addu’a Allah ya ba wa Musulmi dama su halarci ibadun watan Ramadan tare da samun albarkar da ke cikinsa.

Haka nan, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci masu hali da su tallafa wa mabukata kafin, yayin, da bayan Ramadan, musamman a irin wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi ya bukaci masu hanni da shuni su taimaki mabukata a watan azumi Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Sultan ya ja hankalin ƴan kasuwa

Ya kuma gargadi ‘yan kasuwa da su guji ajiyar kaya da kara farashin kayan masarufi domin kauce wa wahalar da Musulmi masu azumi.

A ƙarshe, Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya watau NSCIA ta yi wa ɗaukacin musulmin Najeriya da na duniya fatan alheri da murnae zuwan watan Ramadan.

Sai dai da Legit Hausa ta tuntuɓi wani ɗan kasuwa mai shagon saye da sayarwa, Kamala Bello ya tabbatar da cewa kaya sun sauka amma kamar yadda ake yaɗawa ba.

Kamal ya shaidawa wakilinmu cewa suna yanke farashin kayayyaki ne daidai da yadda suka sayo a kasuwa.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir: "Abin da ya kamata musulmi su tuna game da ibadar azumin Ramadan"

"Muna iya bakin ƙoƙarinmu amma ka san dole za mu sayar da kaya ne yadda za mu maida uwa da kuma riba, yadda mutane ke yaɗa karyewar farashin kaya ba haka abin yake ba."
"Ni a karan kaina ina iya bakin ƙoƙari na naga na sawwaƙa ma al'umma ko dan wannan wata da muka shiga na Ramadan, Allah ya sa mu ga karshensa lafiya."

Yadda ake tantance rahoton ganin wata

A wani labarin, kun ji cewa wani dan kwamitin ganin wata a fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yadda suke tantance labarin ganin wata idan mutane suka kai rahoto.

Malam Simwal Jibril ya ce a baya an samu matsaloli da rudani kan batun ganin wata, musamman idan aka samu sabanin ra’ayi tsakanin mutane daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262