Sheikh Jingir: "Abin da Ya Kamata Musumi Su Tuna game da Ibadar Azumin Ramadan"
- Shugaban majalisar malamai na ƙungiyar JIBWIS da aka fi sani da Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ja hankalin musulmi
- Babban malamin ya yi kira ga ɗaukacin musulmi su tuna cewa Allah ya wajabta azumin Ramadan ne don ya jaraba imani da biyayyarsu a gare Shi
- Jingir ya kuma nuna damuwarsa kan tsadar kayan abinci, ya buƙaci ƴan kasuwa su ji tsoron Allah, su tausayawa al'umma a wannan lokaci mai albarka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, Plateau - Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedkwsta a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi nasiha kan azumi.
Fitaccen malamin ya bukaci Musulmi a duk fadin duniya da su ji tsoron Allah, su tuba, kuma su tsarkake ibadarsu ba kawai a lokacin Ramadan ba, har da bayan watan.

Asali: Facebook
Sheikh Sani Jingir ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin taron shekara-shekara karo na 32 da kungiyar Izala ta Jos ta shirya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Sani Jingir ya faɗi manufar azumi
Ya jaddada cewa azumin watan Ramadan ba azaba ba ce, illa jarrabawa daga Allah don tantance tsoronSa da biyayya a gare Shi.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce:
"Allah ne ya umurce mu da azumi domin Ya gwada imaninku. Saboda haka, kada ku yi azumi don mutane su yaba muku, ku yi shi domin Allah, domin Shi ne ke ganin dukan ayyukanmu."
Ya kuma bukaci Musulmi da su bi dokokin azumi yadda ya kamata, su kuma halarci tafsir a masallatai don kara fahimtar addininsu.
Jingir ya ja hankalin ƴan kasuwa
Sheikh Jingir ya yi Allah-wadai da yawaitar hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, yana mai jan kunnen ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah su sassauta wa al’umma.

Kara karanta wannan
Ramadan: Ɗan majalisa a Arewa ya tara talakawa, ya raba masu kudi da kayan abinci
Ya ce:
"Mutane na cikin halin kunci saboda tashin farashi maras dalili. Duk da cewa ana rade-radin cewa farashin kayayyaki ya ragu a kasuwanni, amma har yanzu ‘yan kasuwa sun ki saukewa.
"Wannan rashin adalci ne, kuma ina kira gare ƴan kasuwa musamman masu shaguna su da su ji tsoron Allah."

Asali: Facebook
Najeriya na bukatar addu'o'i
Daga karshe, Sheikh Jingir ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’a domin zaman samun dawwamammen lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Babban malamin ya ƙara da cewa addinin musulunci na koyar da hadin kai da son juna, don haka kowa ya tashi tsaye don ciyar da kasa gaba.
JNI ta buƙaci malamai su haɗa kansu
A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar JNI karkashin sarkin Musulmi ta buƙaci malamai da shugabannin addinin musulunci su haɗa kansu, su cire son zuciya.
Da yake jawabi a taron laccar Ramadan da JNI ta shirya a Kaduna, Sultan Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga masu wa'azi su gujewa fatawowin da za su raba kan al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng