Ramadan: An Yi Bikin Karya Farashin Kayan Abinci a Jihar Kano

Ramadan: An Yi Bikin Karya Farashin Kayan Abinci a Jihar Kano

  • A wani biki na musamman da aka shirya a Kano, an rage farashin kayan abinci domin rage wa jama’a radadin matsin tattali
  • Shugabannin kasuwanni tare da goyon bayan gwamnatin Kano ne suka shirya bikin tallafin kayan abinci a jihar
  • Masu sayayya sun yaba da rangwamen, inda wasu suka ce sun samu saukin kashi 10% zuwa 15% a kan kayan da suka saya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A yayin da watan Ramadan ke karatowa, an rage farashin kayan abinci a Kano domin saukaka wa al’umma ciniki a wannan lokaci na azumi.

Bikin tallafin kayan abinci na musamman da aka shirya a jihar ya samu goyon bayan shugabannin kasuwanni da kuma gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan Najeriya za su yi tirjiya ga Tinubu kan karin kudin wuta

Abinci
An sauke farashin kayan abinci a Kano. Hoto: Hassan Ahmad
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa a bikin, an rage farashin kayan masarufi kamar shinkafa, gari, sukari, alkama, wake, taliya, man girki da kuma doya, domin talakawa su amfana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu sayayya sun yaba da rage farashi

Wasu daga cikin mutanen da suka halarci bikin sayen kayan abinci sun bayyana jin dadinsu game da rangwamen farashi da suka samu.

Aishatu Kyauta, wata mai siyayya, ta ce ta lura cewa an rage farashin kayan da ta saya da kashi 10% zuwa 15%, wanda hakan ya taimaka mata sosai a wannan lokaci na tsadar kaya.

Haka zalika, wani mazaunin Kano, Musa Umar, ya ce ya sayi buhun sukari a kan N79,000 da kuma buhun shinkafa akan N72,000, farashin da ba zai samu a wata kasuwa ba.

An bukaci ‘yan kasuwa su daina boye kaya

A cikin wata sanarwa da sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar, Sarkin Musulmi ya bukaci gwamnati, kamfanoni da masu hali da su tallafa wa mabukata.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun kama 'yan bindiga hannu da hannu, sun kashe su har lahira

Ya kuma shawarci ‘yan kasuwa da su guji boye kaya da kara farashi ba gaira ba dalili, domin hakan zai jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

Ana ganin hakan na cikin amsa kiran sarkin Musulmi da 'yan kasuwar Kano suka yi ga al'ummar jihar.

Kayan abinci
Wuraren sayar da abinci. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: UGC

An gargadi masu daukar nauyin Tafsir

Sarkin Musulmi ya shawarci masu daukar nauyin Tafsir da gidajen rediyo da su yi taka-tsan-tsan da sakonnin da suke yadawa, domin kauce wa tada zaune tsaye.

Ya yi kira da a kiyaye mutuncin addinin Musulunci da kuma hadin kan al’ummar Musulmi a lokacin Ramadan da kuma bayan sa.

Bikin sayar da kayan abinci a farashi mai rahusa yana ci gaba da samun karbuwa, yayin da jama’a ke tururuwa domin amfana da wannan rangwame.

Ana fatan wasu jihohi za su yi koyi da hakan domin samar da sauki yayin da al'umma suka tunkari lamari mai muhimmanci kamar azumi.

Kara karanta wannan

Ramadan: Yadda kayan abinci suka yi sauki a Arewa ana shirin azumi

Farashin abinci ya sauka a jihohi

A wani rahoton kun ji cewa farashin kayan abinci ya karye a jihohi yayin da al'ummar Musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewa an samu sauki a kasuwannin jihohin Kano, Taraba, Benue, Niger da wasu sassa daban daban na Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng