Zanga Zanga: 'Yan Najeriya za Su Yi Tirjiya ga Tinubu kan Karin Kudin Wuta

Zanga Zanga: 'Yan Najeriya za Su Yi Tirjiya ga Tinubu kan Karin Kudin Wuta

  • Gwamnatin tarayya na shirin kara kudin shan wutar lantarki ga 'yan kasa don inganta kudin shigar bangaren a Najeriya
  • ‘Yan kasuwa da kungiyoyin farar hula sun ce ba wata hujja da ke tabbatar da bukatar karin kudin wuta a halin da ake ciki
  • Kungiyoyi sun yi barazanar yin zanga-zanga idan gwamnati ta aiwatar da karin kudin tare da fadin matsalolin da za su fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce tana duba yiwuwar kara kudin lantarki ga masu amfani da layin Band B zuwa kasa domin cike gibin kudin da ake bukata a bangaren samar da wuta.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a yayin gabatar da sabon tsarin wutar lantarki na kasa (NIEP) da shirin amfani da albarkatu (NIRP) a Abuja.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Masana taurari sun fadi ranar ganin watan Ramadan a Najeriya

Tinubu
Kungiyoyi sun yi barazanar zanga zanga kan karin kudin wuta. Hoto: Bayo Onanuga|Bayo Adelabu
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ministan ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin tallafin wutar da ya kai Naira tiriliyan 3 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, bashin da kamfanonin samar da wuta (GenCos) ke bi ya kai Naira tiriliyan 4, wanda ba zai yiwu a ci gaba da tafiya haka ba.

'Kari kudin wuta zai hallaka sana’o’i' - Kungiyoyi

Kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya (ASBON) ta bayyana cewa karin kudin wutar lantarki zai durkusar da kananan sana’o’i a kasar nan.

Shugaban kungiyar, Dr. Femi Egbesola, ya ce mafi yawan ‘yan kasuwa na dogara ne da lantarki, kuma karin kudin wutar zai haifar da hauhawar farashin kaya da raguwar ciniki.

Ya kara da cewa karin kudin wutar zai kara jefa kananan ‘yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki, wanda ka iya haddasa rufewar sana’o’i da dama a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Najeriya ta kafa tarihin kera jirgi a karon farko, zai fara tashi sararin samaniya

Kungiyoyin sun yi barazanar zanga-zanga

Kungiyar kare hakkin ilimi (ERC) ta yi gargadi cewa duk wani yunkuri na kara kudin wutar lantarki zai gamu da turjiya daga al’ummar Najeriya.

Shugaban kungiyar, Hassan Taiwo, ya ce gwamnati ba ta inganta wutar lantarki ba, amma tana kokarin kara kudin amfani da ita, wanda hakan rashin adalci ne.

A cewarsa, har yanzu ‘yan Najeriya na fama da matsalar yawaitar katsewar wuta da kuma gazawar kamfanonin rarraba wuta (DISCOs) wajen inganta hidimarsu.

Ministan makamashi
Ministan makamashin Najeriya. Hoto: Bayo Adelabu
Asali: Twitter

MSA ta yi suka kan shirin karin kudin wuta

Kungiyar farar hula ta MSA ta yi Allah-wadai da shirin karin kudin wutar lantarki, tana mai cewa ana cutar da talakawa ne don amfanar da wasu tsiraru.

Sakataren kungiyar, Dagga Tolar, ya ce tsarin Band-A na karin kudin wuta wata dabara ce da ake amfani da ita domin raba ‘yan Najeriya da juna, tare da bai wa masu hannu da shuni fifiko.

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauke Ganduje a shugaban APC? Sakataren jam'iyya ya magantu

Ya kara da cewa kamfanonin rarraba wuta ba su saka hannun jari a bangaren samar da wuta, sai dai su ci gaba da karbar riba ba tare da yin kokarin bunkasa samar da wutar lantarki ba.

An kori ma'aikatan lantarki a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba wuta na KAEDCO ya sanar da korar ma'aikata yayin da ake tsaka da tsadar rayuwa.

Legit ta rahoto cewa kamfanin ya kori ma'aikata kusan 1,000 wanda ana ganin hakan barazana ce ga rayuwarsu da tattalin kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng