ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, An Rufe Jami'a a Arewa

ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, An Rufe Jami'a a Arewa

  • ASUU ta reshen jami’ar jihar Sokoto ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani saboda rashin magance matsalolin da suka addabe ta
  • Kungiyar ta ce yajin aikin zai shafi dukkanin harkokin jami’ar, ciki har da koyarwa, jarrabawa da tantance sakamakon dalibai
  • Yajin aikin ASUU-SSU na zuwa ne mako guda bayan malaman jami'ar jihar Kaduna (KASU) sun shiga yajin aiki na sai baba ta gani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jami’ar jihar Sokoto ta fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Laraba.

Kungiyar ta ce gazawar mahunkta, kwamitin gudanarwar jami'ar, da gwamnatin jihar wajen magance matsalolin da suka jima suna fuskanta ne ya jawo yajin aikin.

ASUU ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani a jami'ar Sokoto
ASUU ta fadi dalilin shiga yajin aikin sai baba ta gani a jami'ar Sokoto. Hoto: @asuunews
Asali: Facebook

ASUU ta rufe jami'ar Sokoto da yajin aiki

A cikin wata sanarwa, ASUU ta ce za ta tabbatar da cikakken bin umarnin yajin aikin, wanda zai dakile duk wasu harkokin ilimi a jami’ar, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan Najeriya za su yi tirjiya ga Tinubu kan karin kudin wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron da ASUU ta gudanar a Cibiyar Nazarin Halifanci, 'yan kungiyar sun tattauna kan martanin da gwamnati ta yi game da bukatunsu.

Sai dai sun nuna rashin gamsuwa da matsayar gwamnatin, inda suka zarge ta da nuna halin ko in kula da bukatun malaman.

Bayan tattaunawar, ASUU ta sanar da dakatar da dukkanin ayyukan koyarwa, bincike, taruka na hukuma, jarabawa, kula da dalibai, da tantance sakamakon jarabawa.

Kungiyar ta kafa kwamitin sa ido don tabbatar da cewa dukkanin 'ya'yanta sun bi umarnin yajin aikin ba tare da saba ka’ida ba.

Shugaban ASUU-SSU, Dr. Saidu Abubakar, da Sakatarensa, Hassan Aliyu, ne suka sa hannu kan sanarwar da ta tabbatar da shiga yajin aikin.

Yajin da ASUU ta shiga a jami'ar KASU

Yajin aikin na zuwa ne mako guda bayan ASUU, reshen jami’ar jihar Kaduna (KASU), ta fara nata yajin aikin na sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Soyayya ta ƙare: Wani ɗan Najeriya ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta mutu

A wata sanarwa da shugabanta, Peter Adamu, da sakataren reshen, Peter Waziri, suka fitar, kungiyar ta ce an samu amincewar NEC kafin shiga yajin aikin.

Premium Times ta rahoto cewa tun daga ranar 18 ga Fabrairu, 2025, ASUU-KASU ta tsunduma yajin aiki bisa amincewar shugabanninta na kasa.

Dalilin ASUU na shiga yajin aiki

Daya daga cikin matsalolin da suka haddasa yajin aikin shi ne rashin biyan albashin 'ya'yanta da aka dakatar, musamman na watan Satumbar 2017 da 2022.

Haka nan, ASUU ta koka kan rashin biyan alawus na koyarwa tun daga 2016 zuwa yanzu, tare da bashin karin girma da alawus na SIWES.

Kungiyar ta kuma yi korafi kan rashin biyan inshorar rayuwa ga ‘yan kungiyar da suka rasu, tare da rashin aiwatar da karin albashi na 25% da 35%.

ASUU ta bukaci gwamnati ta magance wadannan matsaloli domin kawo karshen yajin aikin da ke barazana ga harkar ilimi a jami’o’in jiharsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wa fulani makiyaya hari, an sace basarake da wasu mutum 38

'Gwamnati ba ta cika alkawari ba' - ASUU

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ASUU ta bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta cika alkawuran da ta dauka ba.

Kungiyar ta ce tun bayan hawa mulkin gwamnatin Bola Tinubu, fiye da shekara guda, ba a warware wata matsala gaba daya ba.

ASUU na shirin gudanar da taro nan gaba domin yanke shawara kan matakin da za ta dauka game da zargin rashin kulawar gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel