Manyan Malaman Musulunci Za Su Shiga Azumi da Nauyi, Gwamna Ya ba Kowane N200,000
- Gwamna Ahmed Aliyu ya ware buhunan masara da kuɗafe domin rabawa limamai, na'ibai, malamai da kungiyoyi albarkacin Ramadan a Sakkwato
- A bayanan da mai girma gwamnan ya yi, kowane limamin Juma'a zai samu buhu biyar na masara da N100,000, na'aibi kuma zai samu buhu uku da N50,000
- Mai girma Gwamna Aliyu ya ce za a ba wasu manyan malamai 300 kowane N200,000 da ƙarin wasu malamai 100 da za a bai wa kowanensu N100,000
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta waiwayi limaman masallatai, na'ibai, ladanai da sauran malaman musulunci.
Gwamnatin ta sanar da ware Naira miliyan 285 a matsayin tallafin Ramadan ga limamai, na’ibansu, ladanai, malamai da kungiyoyin addini a fadin jihar Sakkwato.

Asali: Facebook
Gwamnan Ahmed Aliyu, ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatinsa da ke Sakkwato birnin shehu, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gwamnatinsa ta ware waɗannan kudin ne da nufin rage wa shugabannin addinin musulunci matsin tattalin arziki yayin wannan wata mai alfarma.
Yadda gwamna zai raba tallafin limamai
Gwamnan ya bayyana cewa kowanne limamin Juma’a zai karbi buhuna biyar na masara da kuma N100,000, yayin da na’ibai za su samu buhuna uku na masara da N50,000 kowannensu.
Ya ce ladanai kuma watau masu kiran Sallah za su karbi buhuna biyu na masara da N50,000 kowannensu.
Manyan malaman Sokoto za su karɓi N200,000
Sai kuma manyan malamai 300 da gwamnan ya ce za ba kowanensu N200,000, da ƙarin wasu malamai 100 da za ba kowane N100,000.
A kokarin bunkasa aikace-aikacen addini a matakin karkara, gwamnatin Sokoto ta zabi malaman zaure 10 a kowacee gunduma a kananan hukumomi 23 na jihar da za su samu N50,000.
Bugu da kari, kungiyoyin addini 150 za su samu tallafin N300,000 kowacce, domin ci gaba da ayyukansu na addini albarkacin watan Ramadan.
Gwamna Aliyu ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da karfafa addinin Musulunci a jihar.

Asali: Facebook
Gwamna Aliyu ya buƙaci addu'ar Musulmi
Ya kuma bukaci malamai da al’umma da su yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro a jihar da kasa baki daya.
Daga karshe, ya yi fatan al’umma za su yi amfani da watan Ramadan wajen hada kai, neman gafara, da aikata alheri, yana mai addu’ar Allah Ya sa ayi Ramadan lafiya.
A gobe Asabar, 1 ga watan Maris, 2025 ake sa ran musulmin Najeriya za su tashi da azumi idan har an ga jinjirin watan Ramadan ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu.
Ramadan: Gwamna Radda ya ware N2.3bn
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta ɓullo da shirin taimakawa al'umma a watan azumin Ramadan da ake dab da farawa.
Bayan taron majalisar zartaswa da gwamna Dikko Umaru Radda ya jagoranta, an amince da ware Naira biliyan 2.3 domin wannan shiri na musamman.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng