Sojojin Sama Sun Dura kan Mutanen Gari, An Samu Asarar Rai

Sojojin Sama Sun Dura kan Mutanen Gari, An Samu Asarar Rai

  • Mutanen yankin Barikallahu a jihar Kaduna sun shiga fargaba bayan jami'an sokojin sama sun auka masu da daddare
  • Jami'an sojojin sun kai samame a yankin inda suka hallaka mutum ɗaya tare da raunata wasu mutum biyu a lokacin
  • Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun je yankin ne bayan an samu taƙaddama tsakanin wani soja da wani mutum kan wata mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu sojojin saman Najeriya sun dura kan mutanen yankin Barikallahu, da ke kusa da cibiyar fasahar sojojin sama a jihar Kaduna.

Sojojin saman waɗanda suka mamaye yankin, sun kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu mutum biyu a daren ranar Laraba.

Sojojin sama sun kashe mutum daya a Kaduna
Sojojin sama sun dura kan mutanen gari a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Punch ta cewa wakilinta ya samu bidiyon lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin sama sun farmaki mutanen gari

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ritsa 'yan bindiga a maboyarsu, an kama 'yan ta'adda 20

Bidiyon ya nuna wata mota da aka rina da launin kayan sojoji, mai ɗauke da tambarin rundunar sojojin sama (NAF), tana shiga yankin.

A cikin wani daga cikin bidiyon, an ga mazauna yankin suna guje-guje yayin da sojojin ke matsowa kusa da su.

A wani yanki na bidiyon, an ga jami’an sojojin sun cafke wani mutum, suna dukan sa, yayin da wasu da ke cikin motar suke cewa (saka shi ciki, saka shi ciki).

Wani bidiyo ya nuna sojojin suna harbe-harbe cikin iska kafin rikodin ɗin ya yanke ba zato ba tsammani.

Majiyoyi sun bayyana yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron ramuwar gayya, ya bayyana cewa tun kafin wannan lamari na ranar Laraba, jami’an sojojin sama sun daɗe suna nuna danniya ga mazauna yankin.

Ya ce wata matsala ce ta taso tsakanin wani soja da wani mazaunin yankin, saboda wata mata wanda hakan ya sanya ya gayyato takwarorinsa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun toshe titunan zuwa fadar Aminu Ado Bayero a Kano, an gano dalili

"Harin da aka kai jiya ya samo asali ne daga rikici tsakanin wani soja da wani mazaunin yankin kan wata mata. Bayan hakan, sojan ya ɗauko takwarorinsa, suka fara dukan mutane, suna harbi cikin iska, tare da korar mutane."
"Abin takaici, mutumin da aka kashe bai san komai ba game da rikicin. Harbin bindigar sojojin ne ya same shi, kuma ya mutu.
Daga cikin mutum biyun da aka jikkata, ɗaya an harbe shi a kafa, ɗayan kuma a kafada. Yanzu haka suna asibiti."

Wani ganau, wanda shi ma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana yadda lamarin ya kasance.

"Sojojin sun shigo yankinmu, suka kashe mutum ɗaya, suka jikkata wasu mutum biyu. Sun riƙa harbi babu ƙaƙƙautawa. A gabana yaron ya mutu."

- Wata majiya

Jami'an sojoji suna binciken harin

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar sojojin sama, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya faɗo kan gidajen mutane, Janar da wasu sama da 40 sun mutu

"Yanzu haka ana gudanar da bincike. Kwamandan rundunar na Kaduna yana tattaunawa da mazauna yankin da abin ya shafa."

- Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa

A halin yanzu, mazauna yankin Barikallahu sun fara bukatar a bi musu hakkinsu, kan mutumin da aka kashe mai suna Godwin.

Sojoji sun jefa bam kan fararen hula

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi kuskuren jefa bam kan fararen hula a jihar Katsina.

Bam ɗin da sojojin suka jefa a ƙaramar hukumar Safana, ya yi sanadiyyar rasuwar fararen hula har mutum bakwai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng