Wata Sabuwa: Sanata Natasha Ta Shirya Yin Fallasa kan Takaddarmarta da Akpabio

Wata Sabuwa: Sanata Natasha Ta Shirya Yin Fallasa kan Takaddarmarta da Akpabio

  • Taƙaddamar da ake yi tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ta ɗauki sabon salo
  • Sanatan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa ta bayyana cewa ta shirya yin magana kan dukkanin abubuwan da suke faruwa
  • Natasha Akpoti ta nuna shirinta na fuskantar kwamitin bincike da aka kafa kan taƙaddamarta da Godswill Akpabio a zauren majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sake taɓo batun taƙaddamarta da Godswill Akpabio.

Sanata Natasha Akpoti ta ce ta shirya yin magana dangane da taƙaddamar da ta yi da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kuma wasu abubuwa da dama da suka faru a majalisar.

Sanata Natasha na takaddama da Akpabio
Sanata Natasha na takun saka da Akpabio Hoto: The Nigerian Senate, Natasha H. Akpoti
Asali: Facebook

Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana hakan a shafinta na Facebook a safiyar Alhamis, 27 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

Shirin babban taron APC ya gama kankama, jagororin jam'iyya sun hallara Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shigar da ƙorafi kan Sanata Natasha

Kalamanta na zuwa ne a matsayin martani kan wani ƙorafi da wata ƙungiyar matasan Arewacin Najeriya ta rubuta a kanta, wanda aka miƙawa wani kwamitin majalisar dattawa.

A ranar Talata, majalisar dattawa ta tura Sanatan mai wakiltar Kogi ta tsakiya zuwa gaban kwamitin ɗa'a sakamakon saɓaninta da Godswill Akpabio.

Sanatan dai ta samu saɓani da shugaban majalisar dattawan ne kan batun sauya mata wurin zama a zauren majalisar a makon da ya gabata.

Me Sanatar ta ce kan taƙaddama da Akpabio?

Sai dai, yayin da take mayar da martani kan lamarin, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ta shirya fuskantar kwamitin binciken.

Sanatar ta kuma roƙi ƴan Najeriya da su mara mata baya, tare da jaddada cewa dole ne a watsa zaman binciken kai tsaye a tashoshin talabijin.

"Barka da safiya jaruman mutanen Kogi ta Tsakiya, jihar Kogi da Najeriya baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Akpabio: Shugaban majalisa ya shiga matsala bayan sanata ta maka shi kara a kotu

“Wannan ƙorafin ya zo gare ni a cikin ƴan awannin da suka wuce."
“Kodayake na daɗe ina kaucewa yin magana a fili game da lamarin da kuma wasu abubuwa da suka faru a majalisar dattawa a ƙarƙashin shugabancin Sanata Akpabio, lokaci ya yi da zan yi magana."
“Arise News, ku sanya rana, zan zo ofishinku da kaina. Ku tambaye ni duk abin da kuke so."
“Kuma ga ƴan Najeriya, ku tabbata kun halarci zaman binciken, wanda zan dage sai an watsa shi kai tsaye."
“Kwanaki da makonni masu zuwa za su kasance masu ban sha’awa, amma za su ƙara gyara inganci da ma’aunin shugabanci a Najeriya."

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Natasha ta maka Akpabio ƙara a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ɗauki matakin shari'a kan shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Natasha ta maka Akpabio ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke binrin Abuja kan zargin ɓata mata sakamakon wani rubutu da wani mai taimaka masa ya yi a kanta.

Kara karanta wannan

"Mun inganta tsaro," Shugaba Tinubu ya yi magana bayan El Rufai ya faɗi maganganu

A cikin ƙarar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar a gaban kotun, ta buƙaci kotu ta sanya Akpabio ya biya ta diyyar N100.3bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng