Yaki da Zaman Kashe Wando: Sanata Goje Ya Raba Miliyoyi da Kayayyaki

Yaki da Zaman Kashe Wando: Sanata Goje Ya Raba Miliyoyi da Kayayyaki

  • Sanata Mohammed Danjuma Goje ya rabawa Bayin Allah 700 kekunan dinki tare da kudi N20,000 ga kowane mutum daya
  • Jimillar kudin tallafin ya kai Naira miliyan 14, domin bunkasa sana’o’in hannu da rage radadin talauci da ake fama da shi
  • Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace domin cimma manufar da aka bayar da shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Mohammed Danjuma Goje, ya sake tallafa wa al’ummar mazabarsa ta hanyar raba kekunan dinki da kudi domin bunkasa sana’o’in hannu.

Rabon tallafin ya gudana ne a ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu, 2025, a gidan Sanata Goje da ke Pantami, inda dubban jama’a su ka halarta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Sanata Goje
Sanata Goje ya raba tallafi a mazabarsa. Hoto: Muhammad Adamu Yayari
Asali: Facebook

Hadimin sanatan, Muhammad Adamu Yayari ya wallafa a Facebook cewa an bayar da tallafin ne domin rage radadin talauci da bunkasa sana’o’in a mazabar Gombe ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Danjima Goje ya raba kekunan dinki

Sanata Goje ya raba kekunan dinki guda 700 ga masu kananan sana’o’i, domin basu damar dogaro da kansu da kuma habaka sana’ar dinki a yankin.

Baya ga hakan, ya kuma bai wa kowane mutum da ya karbi keken dinki kudi har naira 20,000 domin taimaka musu wajen fara amfani da kayan aikin.

A cewar Sanatan, wannan tallafi yana cikin shirinsa na inganta rayuwar jama’a ta hanyar bunkasa kananan sana’o’i, wanda hakan zai rage radadin talauci da zaman kashe wando.

Manufar tallafin da Sanata Goje ya bayar

A yayin rabon kayan, wakilan Sanata Goje, Alhaji Danjuma Babayo da Alhaji Abubakar Adamu, sun bayyana cewa an fitar da shirin ne domin tallafa wa mutanen da ke kokarin dogaro da kansu.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun kama 'yan bindiga hannu da hannu, sun kashe su har lahira

Sun ce wannan taimako zai taimaka wajen kara yawan masu sana’ar dinki a mazabar Gombe ta Tsakiya da kuma bai wa matasa aikin yi.

Haka zalika, tallafin zai rage radadin fatara da rashin aikin yi a tsakanin matasa da mata, wanda hakan ke daya daga cikin dalilan matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar nan.

Sun bayyana cewa Sanata Goje ya himmatu wajen ganin cewa jama’arsa sun samu abin dogaro da kansu, shi ya sa yake bayar da irin wannan tallafi.

Kiran Sanata Goje bayan raba tallafi

Sanata Goje ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace domin cimma manufar da aka bayar da shi.

Ya ce manufar rabon kayan ita ce a bunkasa tattalin arziki ta hanyar taimaka wa masu kananan sana’o’i da kayan aiki, ba wai su sayar da su ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wa fulani makiyaya hari, an sace basarake da wasu mutum 38

Sanata Goje
Sanata Goje yayin wani taro. Hoto: Muhammad Adamu Yayari.
Asali: Facebook

Sanatan ya kuma yi alkawarin cigaba da taimaka wa jama’arsa ta hanyar shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki da bayar da tallafi ga masu bukata.

An raba tallafin kudi a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya jagoranci raba tallafin kudi ta hanyar katin ATM ga mabukata.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an zakulo jama'a daga dukkan kananan hukumomi domin cin moriyar tallafin gwamna Umar Namadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng