Najeriya Ta Kafa Tarihin Kera Jirgi a Karon Farko, zai Fara Tashi Sararin Samaniya

Najeriya Ta Kafa Tarihin Kera Jirgi a Karon Farko, zai Fara Tashi Sararin Samaniya

  • Hukumar NASENI ta bayyana cewa jirgin sama na farko da aka kera a Najeriya na daf da kammaluwa, ana shirin gwajin tashi sararin samaniya
  • Injiniya Kareem Aduagba ya ce an yi aikin ne tare da amfani da ci gaban fasahar jiragen sama da ake da su a Najeriya tun a baya
  • Kareem Aduagba ya bayyana haka ne yayin taron wayar da kan jama’a kan fasahar jirgi da kuma yadda hakan zai taimaka wa ci gaban tattalin arzikin kasa
  • An bukaci 'yan Najeriya da su rika amfani da kayayyakin da aka kera a cikin gida domin habaka tattalin arzikin kasar da rage dogaro da kasashen waje

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Hukumar Kayan Fasaha da Kere-kere ta Najeriya (NASENI) ta tabbatar da cewa jirgin sama na farko da aka kera a cikin kasar nan ya kusa kammaluwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Mai jagorantar aikin jirgin saman, Injiniya Kareem Aduagba ne ya bayyana hakan a wani taro da hukumar ta shirya a jihar Kaduna.

Jirgin sama
Najeriya ta fara hada jirgin sama. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar NASENI ta ce ana shirin fara gwajin tashin jirgin saman nan ba da dadewa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana daf da gwajin jirgin saman Najeriya

Shugaban aikin, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa an kan kammala aikin jirgin kuma za a fara gwajin tashi a nan gaba kadan.

Ya ce an hada jirgin ne ta hanyar amfani da wasu sassan da aka samo daga kasashen waje sannan aka kera wasu a Najeriya, domin tabbatar da ingancinsa.

A yanzu haka 'yan Najeriya sun zuba ido domin ganewa idonsu yadda jirgin zai tashi a sararin samaniyar kasar nan.

Masana na ganin hakan a matsayin wata hanya ta kara habaka tattalin Najeriya da rage dogaro da kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Bayan saukar abinci, gwamnatin Tinubu za ta karya farashin kayan gini

Inganta fasahar jirgin sama a Najeriya

Injiniya Abdulfatai Ambali daga hukumar NASENI ya bayyana cewa ana kokarin tabbatar da cewa fasahar kere-kere na taimakawa ci gaban Najeriya.

The Cable ta rahoto cewa ya kara da cewa hukumar tana hada kai da masana da masu ruwa da tsaki domin bunkasa fasahar jiragen sama da sauran na’urori.

Ana ganin hakan zai taimaka wajen samar da sana'o'i da samar da aikin yi ga matasan Najeriya masu fasahar kere kere.

Bukatar amfani da kayan Najeriya

A nasa jawabin, Saleh Kwaru, wanda ya shirya taron, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan kayayyakin da aka kera a cikin gida.

Ya ce ci gaban tattalin arziki yana da alaka da yadda ake amfani da kayayyakin da aka samar a kasa maimakon dogaro da na waje.

Najeriya
Hoton jirgin saman Najeriya. Hoto: Imrana Muhammad.
Asali: UGC

Ana fatan 'yan Najeriya za su rungumi jirgin da ake kera a cikin kasarsu wajen tafiye tafiya domin habaka tattalin kasar.

Kara karanta wannan

"Ba abin da za a fasa," USAID ta fadi halin da tallafawa Najeriya ke ciki duk da zarge zarge

Azman ya musa sayar da jirgi ga Iran

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin jiragen sama na Azman ya musanta zargin cewa ya sayar wa kasar Iran jiragen sama.

Kamfanin Azman ya ce jiragensa sun ziyarci kasar Iran ne domin wasu gyare gyare na musamman kamar yadda doka ta tanada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel