Bayan Rage Farashin Man Fetur, An Fara Maganar Karya Farashin Siminti a Najeriya

Bayan Rage Farashin Man Fetur, An Fara Maganar Karya Farashin Siminti a Najeriya

  • Ministan ayyuka, Injiniya Dave Umahi ya bukaci masana'antun siminti su rage farashin kowane buhu ɗaya zuwa N7,000
  • Umahi ya bayyana cewa Dala ta karye zuwa kusan N1,400, kuma an rage farashin fetur don haka ya kamata siminti ya sauka
  • Ya gargaɗi masana'antun siminti cewa matukar ba su rage farashin kayansu ba, zai kai batun gaban Bola Ahmed Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bukaci masana'antun siminti su rage farashin kowane buhu daga sama da N9,000 da ake sayarwa a yanzu zuwa N7,000.

Umahi ya bayyana cewa farfaɗowar darajar Naira a kasuwar musaya da saukar farashin man fetur, dalilai ne masu ƙarfi da ya kamata su karya farashin siminti a Najeriya.

Dave Umahi.
Umahi ya bukaci a sauke farashin buhun siminti zuwa N7,000 a Najeriya Hoto: Dave Umahi
Asali: Twitter

Ministan ya danganta hakan da manufofin tattalin arziki da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bullo da su, wanda suka taimaka wajen ɗaga ƙimar Naira da rage farashin kayayyaki, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar daukar mataki kan kamfanoni

A gefe guda, ministan ya gargadi kamfanin sadarwa na MTN da kamfanin gini na RCC Nigeria Ltd kan jinkirin da aka samu a aikin titin Enugu-Onitsha

A wata sanarwa da mai taimaka masa wajen yada labarai, Uchenna Orji, ya fitar, Umahi ya ce za su tuhumi MTN da alhakin duk wata matsalar kudi da za ta hana aikin ci gaba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ba za ta amince da karin farashin aiki (VOP) ba har sai an kammala aikin.

Ministan ayyuka ya gana da MTN da RCC

Umahi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da wakilan MTN da RCC, wanda ƙaramin ministan ayyuka, Mohammad Bello Goronyo da babban sakataren ma’aikatar, O.O. Adebiyi suka halarta.

An tattauna batun kudin aikin titin Enugu-Onitsha da kuma wa’adin kammalawa, wanda aka sake tabbatar da ranar 10 ga Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauke Ganduje a shugaban APC? Sakataren jam'iyya ya magantu

Ministan ya jaddada cewa gwamnati ba za ta amince da wani karin kudi a aikin ba kuma RCC dole ne ta bi ka'idojin kwangila, ba wai yin aiki bisa ra'ayinta ba.

An buƙaci karya farashin siminti

Umahi ya ce:

"Ina farin ciki cewa manufofin shugaba Tinubu suna aiki. A yau, dala tana kusa da N1,400. A da, lokacin da dala ta kusan kai N2,000, farashin siminti ya tashi daga N7,500.
"To me ya sa yanzu da aka daidaita farashin canji, siminti har yanzu bai sauko daga N9,500 ba?"

Ya yi barazanar cewa idan masana'antun siminti ba su rage farashin zuwa N7,000 cikin mako guda ba, zai kai kara ga shugaba Tinubu don daukar mataki.

Siminti.
Gwamnatin Tinubu ya nemi a rage farashin siminti zuwa N7,000 Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

Ɗangote ya rage farashin fetur

A wani labarin, kun ji cewa matatar hamshakin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta rage farashin litar man fetur ana shirin fara azumin Ramadan.

A sanarwa da matatar Ɗangote ta fitar, ta bayyana cewa ta ruguzo da farashin kowace lita daga N890 zuwa N825.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262